Kotun Koli Ta Yanke Hukuncen Karshe Kan Rikicin Jamiyyar APC Na Jihar Kano
Kotun Kolin Nijeriya ta bai wa bangaren gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, nasara a kan zabukan shugabancin jam’iyyar APC reshen Jihar Kano.
Channels Tv ta rawaito cewa; Hakan na nufin bangaren tsohon gwamnan Jihar, Mallam Ibrahim Shekarau, ya sha kaye a shari’ar da aka soma bayan baraka ta kunno kai tsakanin bangarorin biyu sakamakon gudanar da zabuka daban-daban na shugabancin APC a Jihar ta Kano.
A wani hukunci da daukacin alkalai biyar da suka zauna a shari’ar, karkashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro, suka yi a yau Juma’a, Kotun ta tabbatar da hukuncin Kotun Daukaka Kara da ya halatta shugabancin bangaren Gwamna Ganduje.
Rikici ya barke ne bayan Sanata Shekarau da wasu ‘yan majalisar dokokin tarayya na jihar ta Kano sun balle daga bangaren Gwamna Ganduje suka kafa abin da suka kira G-7, inda suka zargi Gwamnan da rashin adalci a shugabancin APC.
Hakan ya sa bangarorin biyu kowanne ya gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyar na Jiha.
A bangaren Gwamna Ganduje, an zabi Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC na Kano, yayin da a bangaren Sanata Shekarau aka zabi Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban jam’iyyar.
Yen Nijeriya Bazasu Yafemun Ba Idan Ban Tsaya Takara 2023 Ba – Osinbajo
Wadannan zabuka sun raba kawunan ‘yan jam’iyyar ta APC a a Jihar Kano, wadda ta fi yawan al’umma a arewacin Najeriya. Hasalima rikicin ya kai ga Ganduje da Shekarau sun rika yi wa juna shagube.