Yen Nijeriya Bazasu Yafemun Ba Idan Ban Tsaya Takara 2023 Ba – Osinbajo
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ce ya ci amanar kasa idan bai tsaya takarar mukamin shugaba kasa ba a shekarar 2023 kuma yanada Tabbacin Yen Nijeriya bazamu yafe mishi ba.
Mista Osinbajo ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin wata ziyara da ya kai jihar Ondo, kuma ya gana da gwamnan jihar Rotimi Akeredolu da masu ruwa-da-tsaki na jam’iyyar APC.
Ya kuma ce rike mukamin mukaddashin shugaban kasa da ya yi a wasu lokuta ya ba shi kwarewar da yake bukata domin ya jagoranci Najeriya.
Mutane na mutuwa a kowace rana, saboda haka zai kasance cin amanar kasa idan na yi ritaya kuma na koma Legas ko Ikenne bayan wa’adin mulkinmu. Ban yi wa kasar nan adalci ba, Kuma Nasan Bazasu yafemun ba in ji Osinbajo.
A nasa bangaren, Gwamna Akeredolu ya ce duk da cewa yen deleget masu haqqin zaben fidda Gwani na jihar suna son sa kuma suna mutunta shi, ubangiji ne kawai ke bayar da mulki.
Osinbajo ya sanar da aniyarsa ta neman mukamin shugaban Najeriya a ranar 11 ga watan Afrilu, kuma tun ranar yake kai ziyara sassan kasar yana neman goyon bayan yen kasar na cimma aniyarsa