Yakamata Muyi Gwajin Kwakwalwa Wa Yen Takara Masu Shiga Zaben 2023 – NDLEA
Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Brig. Janar Buba Marwa (rtd) ne ya rubuta wasika zuwa ga shugaban jam’iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu, inda ya bukaci a bai wa jami’an hukumar NDLEA damar gudanar da aikinsu na gwajin ingancin kwakwalen masu neman takara a zabe mai zuwa.
Marwa ya kuma ce zai rubutawa jam’iyyar PDP, da sauran jam’iyyu cewa a ba wa jami’an NDLEA damar gudanar da gwajin kwakwalen ‘yan siyasa masu neman manyan mukamai.