Hatsari-Jonathan Ya Tsallake Rijiya Da Baya
A yammacin yau Laraba ne tsohon shugaban kasar Nijeria Goodluck Ebele Jonathan ya tsallake rijiya da baya yayin da ya yi hatsarin mota a Abuja wanda ya yi sanadiyyan mutuwar wasu mukarrabansa su biyu.
Daya daga cikin masu taimaka masa, wanda ya tabbatar da afkuwar hatsarin, ya ce Jonathan na cikin koshin lafiya.
A lokacin hada wannan rubuta wannan rahoton, an tabbatar ce wa tsohon shugaban ya isa gidansa.