Na Mace Ce Yakamata Ta Mulki Najeriya 2023- Cewar Wata Yer Takara

Na Mace Ce Yakamata Ta Mulki Najeriya 2023- Cewar Wata Yer Takara.

Wata ‘yar takarar shugaban kasa a jam’iyyar APGA, Mrs Angela Johnson, ta ce 2023 lokaci ne da  Nijeriya za ta samu shugaba mace ta farko.

Johnson wacce ke da cocin ma’aikatar jin kai ta Birrtaniya a Nijeriya, ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis a sakatariyar jam’iyyar da ke Umuahia, lokacin ne ta ayyana tsayawa takarar shugaban cin kasa a hukumance 2023 Karkashin tutar jamiyyar APGA.

Mrs Johnson

Ta ce: “Mazajenmu da aka zabe su a mukaman shugabanci a kasar nan sun gaza.

“Duk da cewa an zabe su ne domin su yi aiki wa mutane amma sai ya zama mutanen da suka zabe su ne ke yi musu hidima.”

Johnson ta bayyana damuwarta cewa kasar ba ta samu ci gaba mai dorewa ba tun bayan dawowar mulkin dimokradiyya a shekarar 1999.

“Allah ne zai jibince ni domin dawo da fatan miliyoyin ‘yan Nijeriya, wadanda suka zama marasa galiwu a Nijeriya.

“Allah shi ya kawo shugaban kasa Muhammadu Buhari kan karagar mulki, ni ma Allah zai kaini kan kujerar da nake nema,” in ji ta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button
%d bloggers like this: