Bana neman in zama shugaban Ma’aikatan Tinubu cewar Elrufai
Gwamnan Jihar kaduna, Nasir El-Rufai, yayi watsi da zargin da ake masa na neman kujerar Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Mai jiran gado Bola Ahmad Tinubu.
Elrufai yayi bayanin a jihar Gombe ranar Asabar yayin da yake tattauna wa da yan jaridu.
Hukumar labarai ta kasar Najeriya Ta bayyana cewa Elrufai ya amshi gayyata na bude sabbin gidaje da gwamnati ta gina guda dari biyar da hamsin da kuma ginin service centre na information systems.
Ya bayyana cewa duka mukaman da ake rataya mai a shafin sada zumunta ba Gaskiya bane.
Gwamnan ya bayyana cewa yafi bukatan taimako wajen Cigaban kasa Najeriya da akan wani mukami.
Malam Nasiru yace ba Sai ka samu muqamin gwamnati zaka bada naka taimako ba na Cigaban kasa, a cewar sa ko baya gwamnati zai ba da nashi gudumawa dan Cigaban kasa.
“Bamuyi wannan maganan da Shugaban kasa Mai jiran gado ba akan wannan batu.
“Ina karantawa a jarida akan wannan mukaman da ake zargin za a bani, amma ni ma’aikacin kasa ne”.
“Inaso inga kasa ta Tana samun Cigaba duk gudumawar da zan iya badawa Zan bayar haka.
“Ba sai ina cikin gwamnati ba, kowa na aiki ko da ma’aikatan gwamnati ko zababbun mukamai kowa da irin nashi gudumawa da yake badawa.
Kuma baran daina aiki wajen cigaban kasa ba” cewar sa.
Gwamnan ya fadi saura kwana 22 da barin kujerar, Yace zai huta amma zai bada shawara wa gwamnati Duk lokacin da take bukata.
“ Zan bada shawara wa mutane kamar su gwamna Inuwa Yahya in Suna bukata” ya ce
Akan Shugabancin Tinubu daga 29 ga watan mayu. Elrufai ya kara da cewa mutane barasuyi nadaman zaban sa ba. Kuma za a samu jindadi a karkashin Tinubu.
Daily Nigeria ta rawaito