Labaran Yau

CIRE TALLAFIN FETUR: Tinubu Ya Nemi Majalisa Ta Amince Masa Ya Bada Biliyan 500 Tallafi Ga..

CIRE TALLAFIN FETUR: Tinubu Ya Nemi Majalisa Ta Amince Masa Ya Bada Biliyan 500 Tallafi Ga Yan Kasa

Shugaban na Najeriya ya ce za a fitar da kudaden ne daga dokar karin kasafin kudi na shekarar 2022 na Naira biliyan 819.5.

Shugaba Bola Tinubu ya rubutawa Majalisar Dokoki ta Kasa, yana neman a yi masa gyara ga dokar karin kasafin kudi na 2022.

Tinubu, a wata wasika da ya aikewa majalisar wakilai, ya ce gyaran dda yake neman ayi shi zai baiwa gwamnatin tarayya damar samar da naira biliyan 500 na kayan agaji domin dakile illar cire tallafin da aka samu kan Premium Motor Spirit da aka fi sani da fetur.

Fuel Subsidy
Fuel Subsidy

A zaman da aka yi a ranar Laraba, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya karanta wasikar Tinubu, mai take, ‘Neman gyara dokar kasa ta 2022’.

A cewar shugaban, za a fitar da kudin ne daga dokar karin kasafin kudi na shekarar 2022 na Naira biliyan 819.5.

“Na rubuta ne don neman amincewar Majalisar Wakilai don gyara dokar karin kasafin kudi na 2022.

“Buƙatar ta zama dole a cikin wasu abubuwan da ake buƙata don samun kuɗin da ake buƙata don samar da abubuwan jin daɗi don rage tasirin cire tallafin man fetur a kwanan nan ga ‘yan Najeriya.

“Don haka an ciro Naira biliyan 500 kacal daga cikin karin kasafin kudi na shekarar 2022 na Naira biliyan 819.536 don samar da kayan agaji ga ‘yan Najeriya don dakile tasirin cire tallafin mai. Ina fatan majalisar wakilai za ta yi la’akari da bukatar,” a cewar wasikar.

Hakan na zuwa ne kimanin makonni shida bayan da Tinubu ya bayyana cewa an kammala biyan tallafin man fetur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button