Labaran Yau

YANZU YANZU: Shugaban Sojin Tsaro Ya Gana Da Gwamnan…

YANZU YANZU: Shugaban Sojin Tsaro Ya Gana Da Gwamnan Zamfara A Sirrance

Babban Hafsan sojinTsaro, Maj.-Gen. Christopher Musa, da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal suna wani taro a yanzu haka a hedikwatar tsaro dake Abuja.

Duk da cewa har yanzu ba a bayar da cikakken bayani game da taron ba, zuwa lokacin da aka gabatar da wannan rahoto, an gano cewa ganawar da za a yi za ta shafi matsalolin tsaro da suka addabi jihar ta Zamfara.

Lawal, wanda ya isa shelkwatar sojojin da misalin karfe 12:22 na rana yana tare da hadimansa da bayanan tsaro, yayin da babban hafsan tsaron ke gefensa da wasu manyan hafsoshin soji dake cikin rukunin sojojin.

Wani jami’in da ba ya son a buga sunansa, ya shaida wa mana cewa, idanunsu na kan sojoji su shawo kan matsalar ‘yan fashi da makami a Jihar Zamfara har abada, shi ya sa aka yi taron.

Gen Christopher
Gen Christopher

“Baya ga sakon taya murna da dukkansu za su yi musanyarwa, za su kuma tattauna dabarun yadda za a magance matsalolin tsaro a Jihar Zamfarar da ma sauran jihohin kasar nan,” in ji jami’in.

Jihar Arewa maso Yamma dai ita ce yankin da ake fama da kashe-kashe, na baya-bayan nan dai shi ne mutuwar ‘yan sanda hudu a wani hari da aka kai a jihar.
‘Yan bindiga sun yi ta kai hare-hare a jihar a cikin ‘yan shekarun da suka gabata – ci gaban da ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane tare da tilastawa da yawa barin gidajen su da dukiyoyin su.

A kwanakin baya wani tsohon gwamnan jihar, Sani Yerima, ya bukaci shugaban kasa, Bola Tinubu ya tattauna da kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke aiki a jihar Zamfara da sauran sassan Arewa maso yammacin kasar nan.

Yerima ya ce tattaunawar da ya ke yi, ta yi daidai da abin da gwamnatin tsohon shugaban kasa Umar Yar’adua ta yi da tsagerun Neja-Delta, wadanda suka haifar da shirin yin afuwa wato Amnesty Program.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button