Saudiya Zata Samar Da Abincin Buda Baki Na Azumi Wa Kashe 34
Kasar Saudiyya za ta kaddamar da wani shirin buda baki a kimanin kasashe 34, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ya ruwaito a ranar laraba.
Hukumar yada labaran ta rawaito cewa, manufar shirin shi ne samar da abincin buda baki ga Musulmi a cikin watan Ramadan, wanda ake fatan soma wa a ranar 2 ga watan Afrilu.
Ana sa ran mutum miliyan 1.2 za su ci gajiyar shirin.
Rahotannin sun ce Ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci, ta yi dukkanin shirye-shiryen da suka wajaba domin ganin shirin ya shafi bangarorin duniya, ko da yake Hukumar tace ya dogara daga yanayin kasashe dake neman bukata.
Za a aiwatar da shirin ne tare da hadin gwiwar ofisoshin jakadancin Saudiyya da cibiyoyin addinin Musulunci na ma’aikatar.