Gomnatinmu Tayiwa Yen Nijeriya Goma Ta Arziki – Buhari
A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta yi wa kasa da yen kasa goma ta arziki, musamman a bangaren bunkasa noma da ababen more rayuwa da sadarwar kimiyya da kirkire-kirkire ga al’ummar Nijeriya.
Buhari ya kuma tabbatar wa yen Nijeriya cewa zai ci gaba da jajircewa wajen dora ka’idojin dimokaradiyya a cikin harkokin siyasa da kuma harkokin mulki.
Da yake jawabi a lokacin da ya karbi bakuncin Sanata Abdullahi Adamu, zababben shugaban jam’iyyar APC na kasa, Buhari ya ce, “A yau, ya kamata mu yi farin ciki da cewa jam’iyyar mu ta samu jinyar raunukan da ta samu, ta kuma warke yadda ya kamata, ta yadda zata tunkari kalubalen dake barazana ga jam’iyyar a zabukan jiha da na kasa baki daya,” in ji shugaban a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar.
Lokacin da na yi tunani a kan ayyukan da muka shimfida a kasa, musamman akan tattalin arziki da fannin noma, samar da ababen more rayuwa, kimiyyar sadarwa da kirkire-kirkire da kuma matakan jin dadin da muka sanya wa mata, matasa da marasa galihu a cikin al’umma, na samu sabon kwarin gwiwa cewa yen kasarmu za su ci gaba da marawa jam’iyyar APC baya a yakin zabenmu.”
Gwamnatinmu tana aiki ne domin ci gaban kasa, manufofinmu da shirye-shiryenmu ba komai ba ne illa ci gaban kasa da al’ummarta, a hakikanin gaskiya ya kamata jam’iyyar ta sake sanarwa wa ‘yan kasa shirye-shiryen gwamnatin domin kara bawa jama’ar kwarin gwiwar sabe zaben Jam’iyyar ta APC.