Labaran Yau

EFCC Ta Kara Kama Mompha Kan Halatta Kudin Haram Naira Biliyan 6

EFCC ta kara kama Mompha kan halatta kudin haram Naira biliyan 6

Hukumar kula da laifin kudi ta kasa EFCC ranan litinin ta kama wanda ya shahara a shafin sadar da zumunta Ismail Mustapha wanda aka fi sani da Mompha, da laifin hallata kudin haram na kimanin naira biliyan Shida.

Jami’in EFCC, Sulaiman Sulaiman ya bayyana wa kotun da ke zantar da hukunci wanda ya samu hadin kai da jami’an kasa da kasa wajen kara garkame Mompha.

“Hukuncin zai kawo ma Mai yanke hunkuncin da hadin kan jami’an kasa da kasa. Wanda yayi silar garkame shi.

DOWNLOAD ZIP/MP3

“Mun shiryq kulle shi Kamin mu kawo shi gaban kotu dan yanke masa hukuncin da ya dace.

“Lauya mai kare shi ya bayyana min cewa yana neman a daga zaman dan bare samu halartan zaman ba” inji Sulaiman.

Mai shari’a Mojisola Dada ya daga zaman zuwa ranan uku ga watan juli dan cigaba da zaman.

Kotun ta bayyana ran 21 ga watan satumba a shekarar 2022 dan fara zaman, amma mai kare kansa bai halacci zaman ba.

Hukumar labarai ta kasa ta bada rahoton cewa EFCC ta ta kama Mompha da abokan aikin na kampanin Ismalob Global Investment akan laifi 8 kan halatta kudin haram naira biliyan 6, wanda ya bayyana cewa ba haka bane Kuma baiyi laifi ba.

Kotun ran 22 ga watan satumba shekarar 2022 ta bada daman kama Mompha bayan rashin halartan zaman kotu.

Hukumar labarai ta kasa ta nuna cewa Mai shari’a Dada ta katse belin wanda ake tuguma.
Kuma bai halarci zaman kotu na ranan sha shida ga watan yuni na shekarar da ta gabata ba.

Ran goma ga yuni, 2022. Efcc ta na tugumar sa da kin zuwa kotu wanda aka gano ya fita kasar Dubai da wata paspo na kasa da kasa.

Tugumar da akeyi wa Mompha harda halarta kudaden da aka samu ta haramtaccen halkalla.

Wasu daga cikin laiifukan sa sun hada da, amfani da kayyaki wanda aka samu ta haramtaccen hanya, da kuma takardun karya wanda babu dukiyar a bayyane da kuma rashin bayyana dukiyar sa.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button