Labaran Yau

Sojoji Sun Dakile Harin Da ‘Yan Ta’adda Suka Kai Masu A Zamfara

Sojoji Sun Dakile Harin Da ‘Yan Ta’adda Suka Kai Masu A Zamfara

Dakarun Operation Hadarin Daji, a daren ranar Litinin, sun dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kan sansanin sojojin.

Sojojin sun kuma kwato bindigu guda bakwai, alburusai, da babura shida daga hannun ‘yan fashin.
Sojojin sun kuma kashe ‘yan bindiga akalla bakwai a arangamar da suka yi a yankin Kango Sabuwal da ke karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.

Dakarun rundunar ‘Sector 1’ Operation Hadarin Daji tare da sojojin da aka girke a Forward Operating Base (FOB) Wanke, a yankin gwamnati sun kai harin kwantan bauna akan hanyar da ake zargin ‘yan bindiga ne ke amfani da su.

Wata majiyar sojan da ta so a sakaya sunanta ta shaida wa wakilin mu cewa sojojin sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga akalla bakwai yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Ya ce jim kadan bayan arangamar sojojin sun ci gaba da fafatawa da sauran ‘yan bindigar da suka tsere tare da kwato bindiga guda daya da alburusai da kuma babura guda shida.

A halin da ake ciki, kwamandan rundunar hadin gwiwa na shiyyar Arewa maso Yamma, Operation Hadarin Daji, Manjo Janar Godwin Mutkut, ya yabawa sojojin bisa jajircewa da suka yi wajen tunkarar ‘yan bindigar.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button