Labaran YauNEWSTrending Updates

‘Yan Zanga-zanga Sunyi Arangama Da ‘Yan Sanda A Abuja

Wasu 'yan zanga-zanga sun tayar da hankali yayin da dan sanda yayi amfani da teargas dan tarwatsa taron a babban birnin tarayya

Zanga-zangar wahalhalun da ake yi a fadin Najeriya, wadda aka fara ranar 1 ga watan Agusta, 2024, wata gagarumar zanga-zanga ce a fadin jihohi daban-daban da nufin magance matsalolin tattalin arziki da kuma al’amuran mulki.

Sai dai zanga-zangar ta dauki wani mummunan yanayi a jihohin Kano, Borno, Yobe, Kaduna, Jigawa, Nasarawa, da dai sauransu, inda ‘yan fashin suka yi amfani da tarzoma wajen kona ababen hawa, da kwashe kayan ajiya, da kuma kai farmaki kan shaguna masu zaman kansu.

Rundunar ‘yan sandan ta bayar da rahoton cewa mutane bakwai ne suka mutu dangane da wadannan al’amura amma sun musanta cewa jami’an tsaro ne ke da alhakin ko daya daga cikin wadanda suka mutu.

Arangama ‘Yan Zanga-zanga Da ‘Yan Sanda A Abuja

Kunngiyoyin yada labarai na yanan gizo sun rahoto cewa wani dan zanga-zanga a Abuja yayi karfin hali ya kalubalanci dan sanda biyo bayan amfani da teargas wajen tarwatsa muzaharar.

Wannan arangama ta faru ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da rashin shugabanci na gari a fadin kasar.

 

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button