ASUU Ta Ballagazar Da Kukan Dalibai Yayinda Ta Qara Tsawon Kwanakin Yajin Aiki
Lallai yan makaranta na cikin haulali na wannan babban matsala da yazama cikas a tsakanin matasa maza da mata. Kungiyar malamai kimiya ta qasa ta qara yanke hukunci akan matsayansu na yajin aiki bayan kebabbiyar zaman da suka gudanar daren9 ga watar mayu.
Labaranyau ta samo ma dalibai isashen bayani kan abinda ASUU ta yanke dangane da komawa makarantar dalibai. Bayani damuka samo daga cewar Shugaban Asuu na Nijeriya baki daya Prof. Emmanuel Osodeke, ranan litinin a wajen gudanar da National Executive Council meeting a cikin ASUU Secretariat dake cikin birnin tarayya Abuja.
A cewar Osodeke, shawarar tsawaita matakin ita ce baiwa gwamnatin tarayya isasshen lokaci domin shawo kan matsalolin da ke tafe.
Ya ce gwamnati ba ta da gaskiya da kungiyar kuma har yanzu jami’anta ba su gana da ita ba. Tsawaita ta fara aiki daga 12.01 na safe, Mayu 8, 2021. Saboda haka sun qara sawon mako 12 nan gaba suna sauraron gomnati wajen biya musu buqatunsu.
Shin meh zaku iya cewa dangane da wannan matsala da ake fama dashi tsakanin ASUU da Federal Govmen?
Chigaba da shigowa shafinmu na labaran yau domin samun ingantattun labarai masu inganci, maana da kuma qayatarwa.