Jinsin Mata 9 Da Allah Ya Tsine Musu Albarka
Annabi SAW ya kira jinsin mata tara da Allah ya tsine musu Albarka, duk tausayin Annabin Allah da yafi kowa tausayi a duniya. In kina ciki, kiyi kokari ki fita aciki da gaggawa dan biki san ranan da zaki mutu ba.
Na farko Allah ya Tsine ma Alwaashima mace mai yin wani zane da mata keyi, ayi ado a fuska ana sanya wasu bakaken abu jiki, da mai sana’ar yi da wanda aka mata duka Allah ya tsine musu. wal waasila da wanda take sana’ar karin gashi da attachment, yanzu sabon yayi da ulu akeyi, Allah yayi ta da gashi kadan tace sai tace wai sai yayi yawa, toh wanda sana’arta kara gashi ne Allah ya tsine mata Albarka.
Na hudu kuma da wanda ta bada kanta a mata attachment Allah ya tsine mata. Na biyar yace Annamisa, mai kankare hakorinta dan tayi wushirya, wal mutanammisa wanda ake kankare mata hakori dan tayi wushirya, duk wannan iyaye mata wasu suna yi, Allah ya kare su.
kuma yace Wal waashira, masu rina gashi, lalle ya halatta amma an tsine wanda takeyin baki da kuma wadda takeyi wa wasu Allah ya Tsine musu.
Almughaiyirat, mai bleaching, masu canza nau’in fatarsu zuwa wani kala. masu canza halittar Allah, Allah ya tsine musu. iyaye mata a duk duniya ba mai jin tausayinmu mu daku fiye da fiyayyen Allah Annabi SAW, duk duniya babu mai tausainmu kamar shi, amma yace Allah ya tsine wa masu wadannan aiyuka.
Wa zai kwace ku idan mai tausayinku yayi wannan magana, Annabin Allah yana bayyana yanda Allah yake jin tausayin mu. hadisi a Bukhari yace mace ce zata iya daukan dan da ta haifa ta jefa a wuta? mata suka ce yaya hakan zai faru a duniya, Annabi SAW yace toh yanda Allah yake tausayinku yafi yadda mace take tausayin dan ta.
Duk da wannan Allah yace ya tsinewa mata Albarka, yau ka duba yadda mata suke bleaching, ga duk wanda yasan illar bleaching yana ganin mace mai bleaching yasan akwai. wajibi ne iyaye mata su kiyaye wannan.
Nasiha garesu iyaye mata shine Zina, zina yafi faruwa da yan mata, bleaching, attachment duka yafi faruwa da yan mata, amma wasu matan auren ma sunayi. wani zai ce ai ba kowanne ke zina ba.
Menene matsayin matan da ta saka turare ta wuce gaban maza? wani abu na zina da ake rainawa akwai gaisawa da maza da mata yafi faruwa ga yan boko, ubanta yana ganin tana jami’a baya damuwa da mai takeyi, sai ta mika wa namiji hanu su gaisa uban na gani bai dameshi ba.
Yau a sakandare ana gaisawa maza da mata, mai matsayinsa a mususlunci, matan da ke gaisawa da namijin da bana ta ba matsayin zina ne, ga hadisi na imamu abu darda rahimatullahi alaih wanda annabi yake cewa ido biyu na zina wajen kallon abinda bai halatta ba, hannaye biyu na zina wajen gaisawa da wanda bai halatta ba, kafafu biyu na zina wajen zuwa inda bai halatta ba, al’aura yana zina shine zina ta asali.
Daga cikin musifar da muke jan kunne wa iyaye mata shine issue na hawa acaba, muna magana akan hawan acaban mace daya amma yanzu yawuce daya, matan musulmai suna 3 in 1 ko 4 in 1 har kan tanki, mai zaki fadawa Allah gobe akan wannan, Annabi SAW yake cewa da jikinka ya shafi jikin macen da ba taka ba, gara a dinke kanka da kusa shi yafi maka mafi alheri, da jikinki ya taba jikin mijin da ba naki ba gara a dinke kanki da kusa shi yafi miki alheri. Allah ya shiryemu yasa mu dace.