Girke Girke

Yadda Ake Miyar Yakuwa Da Ganyen Albasa

Miyar yakuwa da ganyen albasa yana dadine idan akayishi abisa ka’ida kuma aka samishi kayan hadin da yakamata.

Biyoni don samun cikakken bayanin yanda ake girka miyar yakuwa da ganyen albasa na Hausawa.

Kayan Hada Miyar Yakuwa Da Ganyen Albasa

1. Manja

2. Nama

3. Attaruhu

4. Tattasai

5. Albasa

6. Gyada

7. Maggi

8. Gishiri

9. Citta da tafarnuwa

10. Ganyen Yakuwa

11. Ganyen Albasa

Yadda Ake Hada Miyan Yakuwa Da Ganyen Albasa

  • A wanke naman a daura a wuta a daka citta da tafarnuwa asaka.
  • Ayanka albasa asaka sai asa gishiri da Maggie abar namar ta dafu sannan a juye a kwano
  • Sai a wanke yakuwan a tafasa shi tafasa daya sai a dauraye yarage tsami
  • Sa’annan a soya manja a zuba markadadden tattasai, attaruhu da albasa a soya su tare
  • A saka dakakkiyar gyada a soyasu asa Maggie da gishiri sai a zuba naman da aka dafa tare da ruwan naman
  • Asa ruwan sanwan a sa daddawa guda daya sai a rufe tukunyar
  • Bayan ya tafaso yafara kaman minti biyar zuwa bakwai sai a saka ganyen yakuwan da ganyen albasa a rufe bayan minti biyar sai a sauke.

Ana cinsa da kowani irin tuwo.

Ga Bidiyon Yanda Ake Miyar Yakuwa Da Ganyen Albasa

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button