Girke Girke

Yadda Ake Alalen Gurjiya (Okpa)

Yadda Ake Alalen Gurjiya Okpa

Ita Okpa ko alalen gurjiya abinci ne wanda akeyi da gurjiya, kuma mafi yawa Inyamurai(Kabilar Igbo) neh suka fi amfani da ita kuma su suka kirkirota daga kudancin kasar Najeriya.

Ko da yake wasu daga cikin hausawa da yarbawa ma suna Jindadin cin ita Alalen Okpa.

Kayan Hadi Alalen Gurjiya

  • Gurjiya
  • Attaruhu
  • Tattasai
  • Albasa
  • Gishiri
  • Maggi
  • Gishiri
  • Manja
  • Leda Santana
  • Ruwa
  • Sinadarin Dandano
  • Ganyen Albasa [Ba Lallai ba]

Yadda Ake Hadawa

  • Da farko za’a wanke gurjiya sai a kaishi inji a surfe, sai a markada shi da kayan miya wato attaruhu, tattasai, albasa.
  • Sannan a zuba maggi da gishiri kadan, sai a juyashi kafin sai a zuba manja.
  • A gaurayashi da ludayi har sai ya bi jikin markaden sannan a zuba a cikin laida a daura.
  • A samu tukunya a zuba ganye a ciki, Sannan a zuba ruwa.
  • Sai a zuba alalen a leda santana a kulleshi
  • Idan ruwan yayi zafi sai a saka alalen da aka daura a wuta.
  • In ya dahu sai a sauke

Wasu suna cin Alalen Gurjiya da gishiri wasu sukan ci da yajin barkono.

Ga Bidiyon Yadda Ake Alale Da kafan Saniya

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button