Labaran YauNEWSPolitics

Mace Mai Kamar Maza – Hajiya Rakiya Sani Yer Takarar Gomnan Jihar Taraba Na Jamiyyar PRP Ta Kaddamar Da Kudirinta

Mace Mai Kamar Maza – Hajiya Rakiya Sani Yer Takarar Gomnan Jihar Taraba Na Jamiyyar PRP Ta Kaddamar Da Kudirinta.

Mace Mai Kamar Maza – Hajiya Rakiya Sani Yer Takarar Gomnan Jihar Taraba Na Jamiyyar PRP Ta Kaddamar Da Kudirinta.

Yayin Da Ake Fafutukan Ganin Andama Da Mata A Siyasar Nijeriya Hajiya Rakiya Sani Tayi Alwashin Kawo Cigaba Mai Dorewa A Jihar Taraba Idan An Zabeta 2023 A Karkashin Tutar Jamiyyar PRP

DOWNLOAD MP3

Yer Takarar takai Ziyaran Gabatar da kai A Sakatariyar Jamiyyar Dake Jihar Taraba

Read more Labaranyau.com

DOWNLOAD ZIP

A Jawabinta Tayi Alwashin kawo karshen matsalar tsaro da ya addabi jihar, Hajiya Rakiya Sani Tace Bawani Wanda Ya fito da ita ta fito ne da Kanta don nuna kishi dakuma ganin yenda akabar jihar ta Taraba a baya.

Tayi Alwashin idan aka Gwada bada Mulki Wa Mata zasu taka rarwar da Ba’a taba tsammani ba, Abunda Zata Fara yi Shine Hada Kan Malaman Addini Don Kawo Karshen Rikicin Addini, tace zata kawo karshen wahalan tsadar abinci da samarwa Matasa aikinyi.

”A Matsayina Na Uwa Mace Ba Yenda Za’ayi Nabar Matasanmu Kara Zube Suna Lalace Ba Sana’a”

Jigo Kuma na jikin Yer Takarar Hon Kasimu Haruna Dan Takaran Majalisar Jiha Mai Shirin Wakilcin Alummar Mazabar Zing A Majalisar Jihar Taraba Yanuna Jin Da dinshi ganin mace mai kamar Maza ta cire tsoro ta nuna kishin Jihar ta, Wannan Ba karamin Jajircewa bane.
Hon Kasimu Yayi Kira Ga Alummar Jihar Taraba dasu Bawa Hajiya Rakiya Sani Dama Don Jagorancin Jihar A Jamiyyar PRP, Ajawabinshi Ya Nuna Bayar Da Goyon Bayanshi Dana Alummarshi Na Zing Dari Bisa Dari Wa Ita Hajiya Rakiya Sani.

Shuwagabannin Jamiyya Da Na Matasa Sunsamu Halartan Wannan Taro Mai Albarka.

Yen Takarar Kujeran Majalisar Jiha Dana Tarayya Daga Sassan Jihar Ta Taraba Sun Tofa Albarkacin Makinsu,  Tare Da Fatan Nasara Wa Yer Takarar Gomnan Jihar Taraba Hajiya Rakiya Sani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button