Labaran Yau

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Ya Sake Naɗa Ƙananansa Shida A Matsayin Sabbin..

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Ya Sake Naɗa Ƙananansa Shida A Matsayin Sabbin Hakimai

A yau Juma’a 28 ga watan Afrilun 2023 ne Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP, Ya ke naɗa sarauta ga ƙananan sa su shida Ƴaƴan Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Abdullahi Bayero, A fadar Masarautar Kano wanda suka haɗar da…

1 – Maje Abbas Ado Bayero – (Bauran Kano)

2 – Kabiru Ado Bayero Baba Badde – (Santurakin Kano)

3 – Umar Ado Bayero Baban Sokoto – (Yariman
Kano)

4 – Tijjani Ado Bayero Lima – (Zannan Kano)

5 – Auwalu Ado Bayero Sutura – (Sadaukin Kano)

6 – Ado Ado Bayero Andodo – (Cigarin Kano)

Kazalika da yake jawabi Sarki ya yi musu fatan alkairi da zama wakilai nagari masu riƙe gaskiya da amana a masarautar Kano, Muna kira da ku kiyaye jaddada zumunci a tsakanin ƴan uwa domin bin umarnin mahaliccin mu, Allah ya baku gudanar da wannan muƙami bisa adalci da kare mutuncin mu da addinin mu.

Kuma ya ƙara da cewar Allah Ta’ala ya bamu lafiya da zaman lafiya, Iyayen mu da malaman mu da shugabannin mu da suka koma ga Ubangijin mu, Allah ya jaddada musu rahama ya ci gaba da bamu albarkacin su, Idan wa’adin mu ya yi Allah yasa mu cika da imani, Amin Ya Allah.

Daga Anas Saminu Ja’en

Ku cigaba da bin larai a labaranyau.com

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button