Labaran YauPolitics

Zaben 2023: Wani Fasto Ya Bayyana Wanda Zaici Zaben Shugaban Qasar Najeriya 2023

Wani Fasto Ba yi da sukuni har sai ya bayyana Wanda Zaici Takarar Shugaban Qasa

Yanzu haka wani babban fasto wanda ke King of Kings Delivrance Ministry World, wanda yake cikin karamar hukumar Ishielu dake jihar Ebonyi mai suna Emmanuel Chukwudi ya bayyana mafarkinsa, yafito yafadi sunan wanda zai yi nasaran lashe zaben shugaban kasa. A cewarsa, Ubangiji ya yi masa wahayi wanda hakan ya haifar masa da rashin sukuni, ya hana shi samun natsuwa har sai da ya fito ya fadi abin da aka saukar masa.

Fasto Yace An yi masa wahayi

Daga cikin wata sanarwa da Mujallar Jaridar Legit.ng ta samu Fasto ya bayyana cewa Arewa ita za ta ci gaba da rike madafun iko a zaben 2023 mai gabatowa.

DOWNLOAD MP3

Ina da wahayi da dama dangane da zabe mai gabatowa, Allah madaukakin sarki ya bayyana mani karara cewa mulki zai cigaba da zama a hannun ‘yan Arewa, duk da cewa ’yan kabilar Igbo na Gabashin Najeriya suna kokarin tada husuma akan hakan, ayi min wahayin cewa mulki zai ci gaba da zama a Arewa. “kuma na ga Alhaji Atiku Abubakar a matsayin sabon shugaban kasan Najeriya, a shekarar 2023. Wannan ba shi ne karon farko da Ubangiji ya bayyana min haka ba.kuma hakan ya kasance wani nauyi ne da dole sai na sauke shi.
” A jihar Kano Kuwa,na hangi Jam’iyyar su Kwankwaso, The New Nigeria People’ Party (NNPP) cikin babbar matsala. Sannan na hango almubazzaranci da kudade, Dan haka Su dage da addu’a sosai domin lamari ne mai tsanani‘ cewar fasto.

APC ta sake fasalin jadawalin zaben fidda gwani na shekarar 2023

Kwamitin ayyuka da akafi sani da NWC, na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ta amince da sake fasalin jadawalin zaben fidda gwani na zaben 2023.

DOWNLOAD ZIP

An sauya ranar zaben fidda gwani
Bayanin ya fito ne cikin wata sanarwa da Misata Morka ya fitar a Abuja.

“Hukumar NWC ta APC a ranar Litinin, 23 ga watan Mayu, ta amince da sake fasalin jadawalin zaben gwamnoni, ‘yan majalisar jiha, majalisar dattawa da na wakilai,” in ji shi.
Mista Morka ya ce za a gudanar da zaben fidda gwani na gwamnoni, majalisar dokokin jiha, karamar hukuma duk za a gudanar ne a ranar 26 ga watan Mayu.

Ya ce za a gudanar da zaben fidda gwani na ‘yan majalisar dattawa da na kananan hukumomi a ranar Juma’a 27 ga watan Mayu, yayin da ‘yan majalisar wakilai da na kananan hukumomi za su gudanar da zaben fidda gwani a ranar 28 ga watan Mayu, ya kuma jaddada cewar babban taron jam’iyyar na musamman na zaben fidda gwani na shugaban kasa na shekarar 2023 zai gudana kamar yadda aka tsara a ranakun 29 da 30 ga watan Mayu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Abun al’ajabi baya qarewa wani karamin yaro ya sha wani kalan dinkin rigar makarantarsa daga tela, inda aka ga alama telan bai gwada shi ba kafin dinkin Rigar ta makarantar ta yi matukar girma sosai kuma a haka yaron ya ke ta faman tafiya da ita duk da ta lullube kafafunsa.

Kalli Bidiyon Yanda Tela Yaci Mutuncin Wani Dan Qaramin Yaro

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button