Labaran Yau

Gwamnatin Najeriya Ta Zabi Yahuza Imam A Matsayin Rajistaran NBAIS

Gwamnatin Najeriya Ta Zabi Yahuza Imam A Matsayin Rajistaran NBAIS

Gwamnatin Tarayya ta amince da zaben Farfesa Yahuza Imam a matsayin shugaban Rajistara na Hukumar Karatun Arabic da Islamic NBAIS.

A jawabin ranan talata a Abuja daga bakin jagoran zantarwa da gudanarwa Muazu Sambo, Yace matsayin na shekara biyar ne.

Imam, Farfesa na harcen larabcin zamani, daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya karbi karagar a hannun Farfesa Mohammad Shafiu Abdullahi, bayan wa’adin lokacin nashi ya cika.

DOWNLOAD MP3

Sabon rajistara yayi aiki a matsayin darakta da NBAIS zuwa Fabrailu, 2023 kamin ya koma ABU Zaria.

Imam, wanda ya fara aiki, yayi alkawarin gyara ingancin jarabawar irin ta tsarin duniya.

Ya kara yin alkawarin buda hadakaiya da jami’o’i da hukumomi a ciki da wajen Najeriya.

DOWNLOAD ZIP

Burin sa shine ya cewa Najeriya ta samu cigaba wajen ilimi da fasaha.

“Daliban mu Suna matukar kokari a waje, kuma yakamata mu yi Duk abinda yakamata dan mu inganta na mu” inji shi.

Imam ya ce zai kara saka ido akan makarantun Arabiyya da kwalaji, da kawo cigaba da inganta tsare tsaren koyarwa.

Abdullahi, tsohon rajistara ya bayyana cewa sabon rajistara yana da kwazo Kuma malami ne mai Ilimi wanda zai kawo cigaba a NBAIS.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button