Yadda Zaka Samu OTP Na NIMC A Sabo Layi Idan Layin Ka Ya Bata
Sau da dama mutane suna yawan komplen akan cewa suna so suyi amfani da lambar NIN dinsu domin gudanar da wani cike cike kamar na Jamb, NPower, da dai sauransu amma saboda batan da layinsu yayi sai kaga sun gagara samin daman amfani da NIN number su.
Lallai NIN abune meh mahimmanci a yanzu yanda komai sai kanadashi kafin ka iya cikawa online, toh ganin hakan yasa muka samo mafita ma wadanda layinda sukayi rejista dashi a baya ya bata kuma sunaso a tura musu OTP a sabon layinsu.
Wadanda sukeda bukatar login domin printing ko ganin bayanan NIMC naka amma baka da damar yin hakan domin Karasa Number wayar ka
Da yardan Allah idan kabi wadannan hanya zaka samu damar yin login na NIMC APP dinka acikin sauki har ka gudanar da duk abinda kakeson yi.
Ga Yanda Ake Tura OTP Nimc Sabon Layi Idan Layinka/ki Ya Bata
Abu na farko da zaka farayi kashiga A play store kayi download na NIMC APP
Bayan ka dakko shi, sai ka bude ka sanya lambar NIN din da kake son ganin bayanan ta, daga nan za su tura OTP a lambar da aka bude NIN din da ita,
Idan baka da lambar da aka tura OTP din cikin ta, sai ka samu layi mafi kusa da kai ka danna *346*2*NIN# Ka danna alamar kira📞 misali *346*2*22334455667# (za ka sanya lambar NIN din da ka sanya a cikin application din ne)
- Ka tabbatar akwai katin kamar ₦20 ko fiye da haka a cikin sabon layin da ka danna lambobin!
- Idan kayi komai daidai to nan take zaka ga User ID da OTP na wannan NIN din sun bayyana,
- Sai kayi amfani da OTP din a cikin Application din
- Kana sanya wa zai wuce, zai kai ka inda za ka sa password 🔑
- Sai ka zaɓi lambobi guda shida ka sa, ka sake maimaita su, shikenan zai wuce successfully ✅
ABINDA ZAKA/KI LURA DASHI
Lallai sai kayi requesting OTP ta cikin Application din, kafin ka danna lambobin, sannan kuma ka tabbatar baka dauki dogon lokaci tsakanin requesting na OTP din da danna lambobin ba, domin yin hakan zai iya baka matsala
Yanda Zaka Yi Rejistan NIMC