Labaran Yau

Mutum Talatin Aka Kashe Cewar Yan Sanda A Garin…

Mutum talatin aka kashe a Sokoto cewar yan sanda

A ranar lahadi yan sandan sokoto suka tabbatar da kisan mutum 30 a hannun yan ta’adda a karamar hukumar tangaza dake jihar.

A jawabin da ASP Ahmad Rufai, Mai magana da yawun yan sandan ya bayyana cewa yan ta’addan sun kai hari a kauyukan Raka, Bilingawa, Raka Dutse, Jaba, Dabagi, da tsalewa na Cikin karamar hukumar ran Asabar.

A cewar Rufai, kamin su kai harin, mambobin yan bijilan sun ja ma fulanin kauyan Azam akan harin.

DOWNLOAD MP3

“Yayin da yan bijilan suka sun hautsuna har ya kai da sun ma wasu samari duka wanda mafi yawansu fulani ne.

“Bayannan yan kauyen sun nemi taimako, sai suka samu wajen yan ta’adda su 20 wanda suka zo a kan babura” ya ce.

Ya kara da bayyana yan ta’addan sun bi yan kauyukan suka kashe yan bijilan takwas a Raka, bakwai a Bilingawa, shida a jaba, hudu a Dabagi, Uku a Raka Dutse biyu a kauyen Tselawa.

DOWNLOAD ZIP

Yan harin sun kona mototi biyu, bukka shida da Kuma babur kirar Bajaj wanda ake tunanin na yan ta’addan aka samu.

Ahmad ya kara tabbatar da wani harin da aka kai karamar hukumar Gwadabawa, wuraren gabacin Sokoto.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button