Girke GirkeLabaran Hausa

Yadda Ake Girka Miyar Kubewa Ta Zamani

Yadda Ake Miyar Kubewa Cikin Minti Goma

Mutane da dama suna shan miyar kubewa don dadinta ne ba tare da sani amfanin ta ba yawan cin kubewa na daidaita gudun jini a jikin dan adam.

Yana kunshe da wasu muhimman sinadarai masu matukar amfani ga lafiyar dan adam kamarsu vitamin A, vitamin B, vitamin C da sauransu.

Ana amfani da kubewa wajen gyaran jiki yana sa jiki tsantsi, laushi tare da sheki bari de mu koma kan girki kubewa de ya hadu.

Abubuwan da ake bukata

1. Kubewa

2. Manja

3. Tattasai da attaruhu

4. Albasa

5. Nama

6. Daddawa

7. Bushasshen kifi ko crayfish

8. Citta

9. Tafarnuwa

10. Sinadaran dandano (Maggi, Curry, Time Dasauransu.)

Miyan Kubewa
Miyan Kubewa

Yanda ake hadawa

  • Zaki wanke kubewarki tsafi ki tsane ta saiki yayyanka su ki daka a turmi ki kwashe a roba
  • Sa’annan a soya manja da albasa a zuba markadadden attaruhu da tattasai,nama,daddawa,citta da tafarnuwa a soyasu.
  • Sai a zuba zuba ruwan sanwan miyan daidai yanda ake bukata.
  • A dauko bushasshen kifi a wanke da ruwan zafi a gyara a tabbatar an cire duk wasu datti a zuba.
  • A daka crayfish a zuba da sinadaran dandano a rufe tukunyar abar kayan hadin su dafu
  • Bayan komi ya dafu miya ya yada kanshi sai a dakko dakakkiyar kubewar a zuba ana dan jujjuyawa kar ya dunkule
  • Sai a rufe tukunyar abar kubewar ta dafu miyar kubewa ta kammala
  • Sai a tuka tuwon shinkafa ko na gari ya danganta da wanda ake bukata

Ga yanda Ummi tayi nata bayanin kan yanda ake hada miyan kubewa

Yadda ake miyar kubewa me ogbono da shuwaka

Wannan miya ne da yakamata mu na yawan cinsa saboda ya tara sinadarai dayawa da jikin dan Adam ke nema.

Kubewa de munsan wani kayan lambu ne dake da amfani sosai ga lafiya yana kunshe da sinadarai masu amfani sosai haka shima ogbono.

Daya daga cikin muhimmin amfaninsu shine suna daidaita level din sugar a jikin mutum ga masu son rage kiba ma na temaka wajen Kona kitse ga kuma wanke ciki amfanin de suna da yawa

Abubuwan da ake bukata

1. Kubewa

2. Ogbono

3. Shuwaka

4. Manja

5. Attaruhu da tattasai

6. Albasa

7. Daddawa

8. Citta da tafarnuwa

9. Nama

10. Bushasshen kifi ko crayfish

11. Kayan kamshi da sinadaran dandano (Maggi, Curry, Time)

Yanda zaki hada

Zaki wanke kubewarki tsaf ki tsame ta saiki yayyanka su ki daka a turmi ki kwashe a roba.

Sai ki dauko ogbono ki hada shi da crayfish kikai a niko shi idan kina da blender kuma zaki iya nika shi a gida

Sai shuwakan ki gyarashi ki wankeshi dakyau zaki wankeshi ne iyakan yanda kukeson dacin ya fito a miyar.

Sa’annan ki soya manja da albasa sai ki dakko nikakken ogbono da crayfish dinki

Ki debi soyayyen manjan kadan ki zuba akai kidan kwaba shi sai ki ajiye a gefe wannan anayi ne saboda kar ogbonan ya dunkule a cikin miyan anaso komi yayi daidai.

Sai a daura nama a wuta asa citta da tafarnuwa,albasa, sinadaran dandano da kayan kamshi idan yadau dahuwa.

Ki wanke bushasshen kifi ki wankeshi da ruwan zafi ki gyara a tabbatar an cire duk wasu kaya sai ki zuba su dafu tare bayan sun dafu saiki sauke

Sa’annan ki zuba markadadden attaruhu da tattasai da daddawa a sauran manjan da kika soya aka debi na kwaba ogbono idan attaruhu da tattasan sun soyu saiki juye nama da kifin da kika dafa tare da ruwan naman.

Kisa ruwan sanwan miyan daidai yawanda kikeso ki rufe tukunyar

Idan miyar ya tafarfasa saiki zuba kubewar kina dan jujjuyawa da ogbonon tareda shuwakar ki rufe tukunyar abar komi ya dafu

Miya ta kammala sai a tuka tuwon shinkafa ko na gari ya danganta da wanda ake bukata

Bidiyon Yanda Ake Miyan Kubewa Cikin Sauki

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button