
Yau mun kawo muku yadda ake hada cake, zai iya yiwuwa cup cakes ne koh manyan cake ake ya danganta da dalilin da yasa akayi.
Bayan an hada za a iya gasa ta a cikin babban faranti in za ayi bikin birthday, in na suna ne ko biki Ana iya saka wa cikin kananan faranti dan kowa ya samu shi ake kira cupcakes.
Biyo mu a sannu dan ganin yadda ake hada cake a saukake.
Kayan Hada Cake
1. Fulawa Kofi hudu
2. Simas Butter guda biyu
3. Kwai 14
4. Vineger Rabin cokali
5. Sugar Kofi biyu
6. Baking powder cokali daya
7. Baking soda Rabin cokali
8. Flavour duk Wanda kake so

Yadda Ake Hada Cake
- A zuba sugan akwano tare da butter a juyashi ya juyo sosai idan akwai electric mixer ayi amfani dashi, idan babu shi ayi amfani da hand mixer idan yayi za’a ga ya hade jikinshi yayi fari.
- Sai a fasa kwan aciki a juya sosai ya juyu shima sai ya hade sosai.
- Sai asa bakin powder da vanilla extract ko flavour aciki a juya.
- A dunga diban flour ana barbadawa ana juyawa a hankali harsai yayi.
- Yanayin yadda kwabin cake yake ayishi kamar kaurin talge wanda yayi kauri,
- Ba kamar fanke ba anayinshi yadanyi ruwa ruwa kar yakai taurin fanke,
- Sai shafa butter ajikin kwanon cake din a xuba kwallin cake din amma rabi saboda idan ya fara gasuwa yana tashi idan aka cika kwanon cake din ya taso zai zube.
- Daganan sai a saka a oven idan cake yayi za’aji yana kamshi,
- Idan anaso a tabbatar cikin ya gasu sai a soka toothpick aciki idan aka cire shi babu abinda ya makale ajikin toothpick din to cake ya gasu.
Aci dadi lafiya.
Ga bidiyon yanda ake hada cake
Discover more from Labaran Yau
Subscribe to get the latest posts sent to your email.