
Naira ta fadi bayan shiga sabon sati
Kudin Naira ta fadi akan dalar America ranan litinin, wanda ta ke canzuwa a kan naira 464 akan dala 1 daya a kasuwar bayan fage.
Kudin ta fadi a kaso O.36 cikin dari in aka alakanta da yadda aka canza ranan 12 ga watan mayu akan naira 462.
Ta bayyana naira ta fadi a farashin 463.50 akan dala ranan litinin da ta gabata.
Anyi kasuwanci da canji a farashin 467 Kamin ta tsaya a farashin 464.
Canjin farashin ta faru ne cikin kankanin lokaci, bayan anyi siya da siyarwa a farashin naira 460 bayan anyi kasuwan ci.
An kiyasce kudin da akayi halkallar Miliyan hamsin da digo goma ta bayan fage da kuma farashin shiga da fita.