Cikakken Tarihin HON. OLUBUNMI TUNJI OJO
OLUBUNMI TUNJI OJO wanda aka haifa ranar daya ga watan mayun shekarar Alif dubu daya da dari tara tamanin da biyu. An haife shi a garin Oyin Akoko na jihar Ondo, Ya kasance Injiniya, Dan kasuwa, mai kyauta kuma dan siyasa a najeriya.
Shigar sa Majalisan tarayya a matsayin dan Majalisa, ya rike ciyaman na kwamitin Hukumar neja delta.
Ranar 26 ga watan fabrailu 2023 ya sake lashe zaben sa a matsayin dan Majalisa mai wakiltar Akoko north east da north west. Ya ajiye aikin dan Majalisan tarayya bayan shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya zabe shi a matsayin ministan cikin gida ranar 16 ga watan augusta 2023.
Karatun Bunmi Tunji Ojo
Ya samu ilimi na farko a firamaren ansarudeen a garin oyin akoko daga shekarar 1987 zuwa 1990 da kuma Hakda international school a kaduna daga 1990 zuwa 1992 inda ya kammala karatun firamare a universal primary school a Akure a shekarar 1993.
Sai ya wuce FUTA Staff school inda yayi karatun sakandare inda ya zama shugaban dalibai a 1998. Ya samu shiga jami’ar Obafemi Awolowo inda ya karanci Injiniyar wuta da kayan wuta, a shekaransa na uku a jami’ar ya yi transfer zuwa jami’ar North London inda ya kammala karatun sa a shekarar 2005, yayi kuma digirinsa na biyu kan digital communication and networking a wannan jami’ar london inda ya kammala a shekarar 2006.
Ya samu horaswa da certificate goma sha takwas akan fannin ICT a turai kamin ya ya cika shekara 24.
Aikin Tunji Ojo
Kamin ya shiga harkan siyasa ya shahara a fannin ICT inda ya zama shugaban kampanin ICT ta Matrix IT solutions Limited a shekara 24. A matsayin sa na kwararre ya samu takardan horaswa kan hacking and counter measures.
Ya samu horaswa kan CompTIA Network Plus Engineer da kuma Britannia Hardware A+ Management.
A Najeriya, yayi aiki wa bankin duniya da kuma hukumomin gwamnatin tarayya wanda sun hada da PTDF, JAMB, NFVCB, NCDMB, National Health Insurance Scheme Abuja, da NSIA.
Da kuma kwamitoci Majalisan dattawa da Majalisan tarayya, kampanin gas na najeriya, national commission for mass literacy, Adult and non formal Education kadan daga ciki.
Siyasar BTO
A shekarar 2019, ya lashe zaben Majalisan tarayya inda ya wakilci Akoko North east da north west a jam’iyar APC. Yana da daga cikin wanda suka rinjayi mutane dan goyon bayan Femi Gbajabiamila dan zama shugaban Majalisan tarayya cikin kwamitin sabon shiga zuwa Majalisan.
Bayan watanni kadan, shugaban Majalisan Gbajabiamila ya nada shi ciyaman na kwamitin Neja Delta.
Ya jagoranci bincike kan kudi Naira Biliyan tamanin wanda aka nema aka rasa a hukumar NDDC, ya kuma zama na farko da yafara bincike kan ayyukan hukumar tun shekara Ashirin baya.
A watan maris na shekarar 2021, ya kawo doka wanda ya nemi Majalisan tarayya ta amince dan dakile matsalar badakala a hukumar neja delta, a halin Yanzu dokar bata samu amintuwa ba.
Ya riqe mukamai na kwamiti daban daban a majalisan tarayya wanda sun hada da; mamba na kwamitin tsaro da bincike, kwamiti na Local content, kwamiti na Gas resources, kwamiti na hukumar arewa maso gabas, kwamiti na Gidaje, kwamiti na birnin tarayya, kwamiti na ma’adanai na kasa da mahajjata. Bayan ya lashe zabe na shekarar 2023, ya zama darakta janar na takarar Tajudeen Abbas a matsayin shugaban Majalisan tarayya. Kuma shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya nada shi a matsayin ministan tsaro na cikin gida kuma aka rantsar dashi ranar 21 ga watan augusta na shekarar 2023.
Ranar 22 ga watan Junairu na shekarar 2021, ya samu Karramawar dakta na Public administration daga jami’ar Joseph Ayo Babalola Ijebu Arakeji na jihar Osun.
Iyalen BTO
BTO ya nada aure kuma da yara biyu, sunan matan shi Abimbola Tunji-Ojo wanda itama yar jihar Ondo ce.
Karramawar BTO
Ya samu Karramawar Honorary Doctorate Degree in Public Administration daga jami’ar Joseph Ayo Babalola, Ikeji Arakeji, jihar Osun shekarar Dubu biyu da Ashirin da daya(2021).
Ya Samu Karramawar Award of Recommendation as a Distinguished Lecturer at the 1st African and 2nd Nigeria Conference on Adolescent and Youth Health and Development Abuja, Nigeria (2021)
Ya samu Karramawar Nigeria Union of Journalists (NUJ) Ondo State Council As matsayin dan Majalisa mai kyawu (2021)
Ya Samu Karramawar Award Of Excellence by House of Representatives Press Corps in recognition of excellent performance as Dean of Oversight (2021)
Ya Samu Karramawar Transparency and anti-corruption award in recognition of pragmatic disposition to issues of transparency, accountability, and anti-corruption by National Assembly New Media Forum (2021)
Ya Samu Karramawar Southwest First Alert Magazine Merit Award as the best Federal incumbent Honourable Member for remarkable contributions towards the growth and development of the South-West region (2020)
Ya Samu Karramawar Fellow’s award, National Association of Proprietors of Private Schools (2021)
Ya samu Karramawar Gold award of excellence in Community Development by Southwest Nigeria Excellence Awards (2019)
Ya Samu Karramawar Outstanding Leadership award as one of the key actors of the new Niger Delta by the Niger Delta Student Union Government (2021)
Ya samu Karramawar Leadership award of excellence by Not Too Young To Rule Initiative (2019)
Ya Samu Karramawar Africa Value Awards (AVA) as the Legislator of the Year for effective Representation/Community Development (2021)
Ya samu Karramawar 30 most Influential young Nigerians award by the National Youth Council of Nigeria (2019)
Ya Samu Karramawar Award as Pacesetter in Political Representation by Akoko North West Local Government Council, Okeagbe Akoko, Ondo State (2019)
Ya samu Karramawar Sir Ahmadu Bello Platinum Leadership Award of Excellence (2019)
Ya samu Karramawar National Assembly Best Legislator of the year (2020, 2021)
Ya samu Karramawar The Federal University of Technology, Akure (FUTA), Nigeria Award of Excellence (2021)
Ya samu Karramawar Kwame Nkrumah Leadership Award as “Worthy Ambassador of African 2010 Youth” by All African Students Union (AASU)
Ya Samu Karramawar Excellence Award in Students Empowerment by The National Association of Nigerian Students (NANS) 2010