Cikakken Tarihin Yusuf Maitama Tuggar
Yusuf Maitama Tuggar wanda aka haifa ran 12 ga watan maris shekarar 1967, ya kasance dan siyasa ne kuma diplomat ne a Najeriya. Shi ne ministan mu’amalar kasa da kasa, yayi ambasadar najeriya zuwa kasar Jamus daga shekarar 2017 zuwa 2023. Ya kuma riqe kujerar dan Majalisan tarayya daga shekarar 2007 zuwa 2011 ya wakilci Mazabar Gamawa kuma ya nemi kujerar gwamna so biyu a jihar Bauchi.
Karatun Yusuf Maitama Tuggar
Tuggar ya samu takardan digirinsa ta farko a kan mu’amalar kasa da kasa daga kasar Amurka a jami’ar kasa da kasa. Yayi karatu a Jami’ar Bath, kuma Yana da digirinsa ta biyu masters a fannin mu’amalar kasa da kasa a jami’ar Cambridge.
Aikin Yusuf Maitama Tuggar
Bayan ya kammala karatun sa, Tuggar yayi aiki a kampani daban daban kamin ya dawo aikin gwamnati, ya riqe muqamin chief executive officer gidan mai na Nordic Oil da gas. Ya kuma kasance Yana bada shawarwari kan siyasa da tattalin arziki a jaridar najeriya.
Siyasar Yusuf Maitama Tuggar
Yusuf Tuggar ya shiga siyasa a shekarar 2007 inda yayi takarar dan Majalisan tarayya inda ya lashe zaben ya kuma wakilci mazabar tarayya ta gamawa a jihar Bauchi zuwa 2011.
Ya riqe muqamin ciyaman na kwamitin Public Procurement, mamba na kwamitin lura da kashe kashen kudi a fannin mai da gas, kwamitin ilimi, kwamitin lafiya da ruwa, kwamitin raba ofishin shugaban kasa da bada konturagi.
Yayi duba kan wajen kirkiran national council ta public procurement, kuma ya riqe mamba na kwamitin foriegn affairs, kuma yayi deputy ciyaman na kwamiti korafe korafen jama’a, ya kuma kawo dokar rage wulakancin safaran dabbobi a Majalisan tarayya.
Zaben Gwamna Na Yusuf Tuggar
A shekarar 2011, Tuggar yayi takarar gwamna a jihar bauchi a jam’iyar CPC, Tuggar yazo na biyu a zaben bayan zaben yazo da tashin hankali da rikici.
Ya koma jam’iyar APC a shekarar 2013 ya kuma yi takarar gwamna inda yazo na uku a zaben firamare.
Ambasada Zuwa Jamus Na Yusuf Maitama Tuggar
A shekarar 2017, Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabi Tuggar a matsayin ambasadan Najeriya a kasar Jamus. Yayin aikin ambasada da yayi, ya taka rawar gani taron Majalisan dinkin duniya kan canjin yanayi (climate change). Ya kuma taimaka wajen shirya zuwan chancellor na kasar Jamus zuwa Najeriya a watan august shekarar 2018.
A watan maris na shekarar 2020, Tuggar yaje taron tattaunawa wanda akayi da kampanin Siemens a kasar Jamus akan wutan lantarkin Najeriya, shugaban ma’aikatan Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abba kyari ya samu cutar Covid19 a wurin. A lokacin Tuggar yasa aka kulle ofishin su ta Berlin, inda aka gwada shi aka samu bai kamu da cutar ba. Bayan nan Abba kyari ya rasu ranan 17 ga watan Afrailu.
A matsayin sa na ambasada, Tuggar yayi kokari wajen dawo da artifacts na Najeriya daga kasar jamus da kuma Bronze na jihar benin guda 22 wanda ya kai kimanin Pounds Miliyan Dari.
Tuggar ya gama tenuwar sa a matsayin ambasadan jamus ran 21 ga watan august shekarar 2023.
Inda aka rantsar da shi a matsayin ministan Foreign affairs.
Iyalen Yusuf Maitama Tuggar
Tuggar an haifeshi daga cikin gidan siyasa a jihar Bauchi, Mahaifinshi shine organizing sakatare na jam’iya mai ci na Nothern People Congress kamin samun yancin kasa da bayan samun yancin kasa.
Mahaifinshi yayi sanata a second republic.
Maitama Yusuf Tuggar Yana da mata da yara Amma bai bayyana su wa duniya ba.