Biography

Cikakken Tarihin Sheikh Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo, Rayuwarsa, Karatunsa, Aikinsa, Da’awarsa, Littattafansa, Hotunansa

Cikakken Tarihin Sheikh Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo

Shafin labaranyau.com ta kawo muku cikakken tarihin Malami wanda ya shahara a fagen ilimi na addini a kasa najeriya da kuma duniyan ilmi baki daya.

Cikakken Tarihin Sheikh Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo 
Cikakken Tarihin Sheikh Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo

Rayuwar Sani Umar Rijiyar Lemu

Asalin sunan malam Shi ne Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu, wanda aka haifa ranar 1 ga watan Juli shekarar 1970, Malamin addini ne a kasar najeriya wanda ya samu kwarewa a fannin hadisai da tafseer. Ya samu Karramawar kasa ta officer of the order of Niger (OON) a Oktoba 2022 daga Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ilimantar wa da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Karatun Sani Umar Rijiyar Lemu

Karatun Sani Umar Rijiyar Lemu
Karatun Sani Umar Rijiyar Lemu

Dakta Sani Rijiyar Lemu yayi firamare dinsa a khairul bariyya firamare a kano daga shekarar 1978 zuwa 1983, sai ya wuce gaba dan karatun sakandare a Shahuci High school kano inda ya kammala a shekarar 1987, ya kuma wuce school of advanced Islamic studies, Gwale . Ya kammala a matsayin gwarzon aji a shekarar 1989.

Malam ya tafi jami’ar madina, a nan inda ya karanci fasahan hadisai a digirin da ya farko ya kammala da B.A Hadith science da Islamic studies a shekarar 1994.

Ya kuma yi digirinsa ta biyu inda ya kammala da first class M.A Hadith Science and Islamic Studies a shekarar 2000, Saboda sh’awar ilimi mai zurfi da kuma bincike, Malam ya koma karatun digirinsa ta uku wato digirgir a jami’ar musulunci ta madina wanda Allah ya bashi ikon kammala wa a shekarar 2005 da sakamako mafi kyawu.

Malaman Sani Umar Rijiyar Lemu

Malaman Sani Umar Rijiyar Lemu
Malaman Sani Umar Rijiyar Lemu

Malam ya samu karatu da horaswa a najeriya da kasar saudiyya wajen malamai daban daban wanda sun hada da:

  • Malam Hamza Adakawa (Akhdari, Arba’una hadisan, Ishriniya, Hamziyya da sauransu).
  • Mal. Sani Inuwa (Nahwu da Sarfu) Mal. Mahbub Abdulkadir Sumaly (Balaga ta Jamar)
  • Dr. Bashir Hasan (Aadabul arabiya Da fassara )
  • Mal. Aminu Mahe (Seera ).
  • Sheikh Dr. Umar Hawiyya (Tafsir)
  • Sheikh Dr. Faihan Almudari (Fiqh)
  • Sheikh Abdulmuhsin Al-Abbad (Tauhid)
  • Sheikh Dr. Hafiz Alhakami (Musadalahul hadis)
  • Sheikh Dr. Muhammad Nur Saif (Musadalahul hadis)
  • Sheikh Dr. Abdulsamad Abid (Musadalahul hadis)

Aikin Sani Umar Rijiyar Lemu

Aikin Sani Umar Rijiyar Lemu
Aikin Sani Umar Rijiyar Lemu

Malam Sani malami ne a jami’ar Bayero kano, domin malam ya samu horaswa kan Addini da hadisi.

Malam ya koyar da courses daban daban a saudiyya ta inda yayi aiki wajen rubuta takaicaccen littafin minhajussunnah, risaala ta Imam Shafi’i da kuma littafin bulugul maram. Dalibai dayawa sun saurari koyarwan malam, wanda suka shahara cikin daliban malam sun hada da:

  • Sheikh Alhassan Sa’id Jos
  • Sheikh Muhammad Sani Bala Jos
  • Sheikh Dr. Munir Abdallah Jos
  • Professor AbdulRashid Abdulqaniy na jami’ar jihar Gombe
  • Sheikh Rashid Jos
  • Sheikh Shaakir Jos
  • Sheikh Dr. Abdallah Getso Kano na Sa’adatu Rimi Collage of Education Kano
  • Sheikh Abubakar Abbas Kano
  • Sheikh Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo Kano na Kwalajin ilimi Gumel
  • Sheikh Nasir Yahaya malami na makarantar Aminu Kano Ta Shari’a da Legal Studies
  • Sheikh Dr. Abubakar Muhammad Sani Birnin Kudu – Jami’ar tarayya na Dutse
  • Sheikh Dr. Muhammad Muslim Ibrahim Jihar – Mataimakin Farfesa a jami’ar Al-Qalam  Katsina
  • Sheikh Dr. Ibrahim Abdullahi Sani Rijiyar Lemo – Jami’ar Bayero  Kano
  • Sheikh Dr. Abdallah Usman Kano na jami’ar Bayero Kano
  • Sheikh Dr. Umar Garba Dokaji Gombe
  • Sheikh Dr. Ibrahim Disina Bauchi – MD Sunnah TV
  • Sheikh Yahaya Rabi’u Kura
  • Sheikh Murtala Da’a – Sokoto
  • Sheikh Muhammad Kabiru Maru Zamfara – Darakta Ibn Uthaimin Islamic Center Zamfara
  • Sheikh Dr. Muhammad Kabiru Goje Kebbi
  • Sheikh Muhammad Kabiru Salis Katsina
  • Sheikh Muhammad Basiru Kano
  • Sheikh Dr. Shuaibu Jibril Jos

Littattafan Sani Umar Rijiyar Lemu

Littattafan Sani Umar Rijiyar Lemu
Littattafan Sani Umar Rijiyar Lemu
  • Dhawabit al-Jarh wat Ta’dil inda Al-Hafiz Az-Zahabi, (M.A thesis, wanda aka wallafa a kasar London, U.K 1995)
  • Bita da tahkikin Littafin Al-Ighrab na Al-Imam An-Nasa’i, wallafar a Al-Ma’athir, Madina, K.S.A. a shekarar 1995.
  •  Bita da tahkikin Littafin At-Tamyiz Fi Talkhis Takhrij Ahdith Sharh Al-Wajeez, na Al-Hafiz Ibn Hajar Al-Athqalaani, wallafar Adhwa’ As-Salaf, Riyadh, K.S.A a shekarar 2005.
  • Makarantar Hadith a garin Makkah da Madinah a karni na farko da na biyu da kuma tasirinta a kan ilimin hadisi. (Wanda aka wallafa cikin harshen larabci) (An buga a Darul Minhaj, Riyadh a shekarar 2005)
  • Ra’ayoyi biyu masu hannun riga, na Abul Hasan Ali An-Nadwy (an rubuta da harshen Hausa). (Wanda aka wallafar a Kano, Nigeria 1999). An sa ke bugashi a shekarar 2022
  • Mahimmancin Sunnah a yaren Hausa. (An rubuta a harshen larabci) (Wanda aka Wallafar a King Fahd Qur’an Complex, K.S.A.  a shekarar 2004.
  • Littafin Ayyami Ma’a Daa’iyatil Jeel, wAnda aka Wallafa a kasar Masar a shekarar  2011. Ya kunshi bayanin rayuwarsa tare da marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam
  • Littafin Bughyatul Mushtaq Fi Sharhi Risalati Shaikhil Islam Ibn Taimiyya Ila Ahlil Iraq, wallafar a kasar Masar a skekarar 2013.
  • Littafin Nabiyyur-Rahmah, (Sirar Annabi Muhammad S.A.W) (Wanda aka Wallafa a kasar Masar a shekarar, 2012, 2013 da kuma 2014).
  • Littafin At-Tabseer Li Majaalisit  Tafseer, (an wallafar Egypt, 2012, 2013).
  • Littafin Asheikh Usman bn Fodiye: Qiraa’tun Fee Turathihil Elmi an wallafar a kasar Masar a shekarar 2015.
  • Littafin Tamamu Attahfiq Fi Siratus Saddiq, (Tarihin Sayyadina Abubakar AS-Siddiq R.A ) (An wallafar a Kasar Masar, 2015)
  • Littafin Al Al-maniyyah wa Atharuha fil Mujtama’atul Islamiyya (An wallafar a kasar Masar a shekarar, 2015).
  • Littafin Al Bina’ Al- Ilmi Liddaa’iya (Wanda aka wallafa a kasar Masar a shekarar 2015).
  • Ithafus Sami’ Wal Qari’ Fi Khatm Saheehul Bukhari, (An buga a Nigeria a shekarar 2018).
  • Littafin Bughyatul Muhtaj Fee Khatmi Saheehi Muslim bn Al-Haj, (Wanda aka wallafa a Nigeria a shekarar 2019).
  • Fayyataccen Bayani Na Ma’anoni Da Shiriyar Al’Kur’ani, (Tafsirin AlQur’ani a harshen Hausa ) (An Buga a Bairut Lebanon 2020).
  • Littaffin Fatawoyin Rahama (Wanda aka wallafa a Nigeria a Shekarar 2021
  • Littafin Ramadaniyyat (Takaitattun rubuce-rubuce da ake gabatarwa a kowace rana a Watan Ramadan ) wanda aka wallafa a Nigeria a Shekarar 2021.
  • Littafin Addibajah Fi hukmi Ta’adudil Masaajid min gairi haajah – Littafin dake jan hankali kan yawaitar Masallatan Juma’a ba tare ta bukata ba (Ba a kai ga buga shi ba zuwa yanzu)

Da’awar Sani Umar Rijiyar Lemo

Da’awar Sani Umar Rijiyar Lemo
Da’awar Sani Umar Rijiyar Lemo

Babban Malami a fannin addinin musulunci na Jami’ar  Alkalam dake Katsina daga shekarar 2006 zuwa shekarar 2012, Babban Malami a fannin addinin musulunci na Jami’ar Bayero dake Kano daga shekarar 2013 zuwa yanzu, Shugaban kwamitin daukar sababbin mambobi na hadaddiyar kungiyar malamai ta Karatun afirka a fursuna wanda jami’ar madina ta dau nauyi domin bunkasa ilimin addini.

Karantarwa  da jami’ar madina take gabatarwa ga malaman Arabiya da darusan addinin Musulunci a Maiduguri, Kano da Bauchi.Babban Daraktan Cibiyar Fassara da Bincike ta Imamul Bukhari, (Al-Imamul Bukhari cibiyar Bincike da fassara) Kano. Limamin Babban Masallacin Juma’a na Dorayi, Kano. Shugaban Cibiyar Tattara Karatuttukan Sheikh Ja’afar (Sheikh Ja’afar Islamic Documentation Centre (SJIDC).

Shugaban Cibiyar Tarihin Cigaban addinin Musulunci da kuma tattaunawa tsakanin addinai dake Jami’ar Bayero, Kano (Centre For Islamic Civilization and Interfaith Dialogue (CICID).

Inda Malam Yaje Domin Taron Ilimi A Duniya

Inda Malam Yaje Domin Taron Ilimi A Duniya
Inda Malam Yaje Domin Taron Ilimi A Duniya

Malam yaje taro daban daban a duniya wanda akayi domin bunkasa ilimin addini, fara daga kasa najeriya, Sudan, Mali, saudiyya da sauransu.

  • Taron kasa da kasa kan Sunnah da Sirah, shiryawar  Ministirin musulunci, K.S.A. Yayi magana akan (Muhimmancin dake tattare da Sunnah A adabin hausa) ( Madinah, 2004).
  • Taron kasa da kasa dan koyon bayan Manzon Allah  (S.A.W), shiryawar jami’ar Khartum, da kungiyar Al-Muntada, Al-Khartum, Sudan, yayi magana kan ( Matsayin Manzon Allah cikin sahabbai da sauran Al-ummah. (Sudan, 2007).
  • Bamako Dan muhimmancin da’awa ta media, wanda akayi ranar 20 zuwa 24 na watan Juli,Shekarar 2010 yayi jawabi kan (Media participation: Its importance and Criteria).
  • The regional Conference ta  Da’awa a Sudan karkashin theme na “Adda’iya Al-Mutamayyiz” Khartum, 19 zuwa -23  na watan Oktoba 2014, yayi jawabi  kan: “Al-Bina’ul Ilmi Lidda’iya” (making a solid Academic background for Islamic Preacher”.
  • International Islamic Conference of Security Stability in the Face of Contemporary Challenges organized by Muslim World League with Cooperation of J.I.B.W.I.S Nigeria Wanda akayi  a Abuja Tsakanin 16 zuwa 19  March 2016, yayi jawabi kan (Al-Ghuluw: Asbabuhu wa Ilajuhu).
  • Taron Shugabanci wanda aka shirya na Al-Muntada Al-Islamiy, Ya faru a Khartoum Sudan tsakanin 10th zuwa 14th April 2016, (At-Taurisul Qiyadiy fi Garb Ifriqiyyah: Tajarub wa Tahadiyyat “Shugabanci A afirka ta yamma : Misali da kalubale”).
  • The International Union of Muslim Preachers organised the Conference on the Protection of Societies, which took place in Doha, Qatar, from March 2–4, 2016. The organization’s paper, “The Protection of the Society from the Dread Beliefs: Shi’a in Nigeria,” was presented.
  • International Conference on Islamic and Challenges of Development in the 21st Century Organized by Departmrnt of Islamic Studies and Sharian in Collaboration with Centre for  Qur’anic Studies Bayero University Kano Nigeria, Presented Paper Titled (Al Al-maniyyah wa Atharuha fil Mujtama’atul Islamiyya “Secularism and its Impact on the Muslim Societies”).
  • International Conference on Islam in Africa: Combating Extremism and Terrorism organized by International Moderation Forum in Hashimite kingdom of Jordan, in Cooperation with the Islamic peace Society and the Nigerian Centre for Arabic Research, Paper Presented Titled: “Advancing peace by establishing the Al-Wasatiyya and avoiding the extremism”, Held between 8th to 9th August 2015.

Dakta Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo yana rayuwa da iyalinsa a jihar kano inda yasa karatu da ayyukan da’awah a gaba.

Karatun Da Malam Keyi A Yanzu

Karatun Da Malam Keyi A Yanzu
Karatun Da Malam Keyi A Yanzu
  • Darasin Tafsirin Al-Qur’ani a Masallacin Usman Bin Affan, Kano
  • Darusan Tafsirin Al-Qur’ani a watan Ramadan a Masallacin Gwallaga na Jahar Bauchi
  • Darasin Adda’u Waddawa’  a Masallacin Modibbo Jihar Katsina
  • Darasin sharhin littafin Kalimatul Ikhlas a masallacin Kerau dake Jihar Katsina
  • Sharhin Takaitaccen Littafin Sahihul Bukhari duk ranar Asabar a Masallacin Usman bin Affan Gadon Kaya
  • Darasin Littafin Akida duk ranar Litinin a Masallacin Usman Bin Affan Gadon Kaya
  • Darasin sharhin Manzumar Imam Suyudi ta Ilimin Hadisi a Jihar Bauchi
  • Shirin Fatawoyin a gidan Talabijin da Rediyo a Jihohin Kano (Rahama Radio), Kaduna (DITV) da Jigawa (Radio Jigawa)

Wasu Daga Cikin Karatun Malam

Hotunan Sani Umar Rijiyar Lemo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button