Biography

Cikakken Tarihin Justice Haruna Tsammani, Rayuwarsa, Karatusa, Aikinsa, Iyalensa, Arzikinsa, Shafin Sadarwansa, Hotunansa

Cikakken Tarihin Justice Haruna Tsammani 

Labaranyau.com ta kawo takaicaccen bayani akan rayuwa, aiki da sauransu na haruna Tsammani.

Cikakken Tarihin Justice Haruna Tsammani 
Cikakken Tarihin Justice Haruna Tsammani

Rayuwar Haruna Tsammani

Justice Haruna Tsammani ya kasance lauya ne kuma Alkali, an haifeshi ran 23 ga watan nowamba shekarar 1959 a jihar gombe kuma shi dan Tafawa Balewa ne karamar Hukuma a jihar Bauchi.

Karatun Haruna Tsammani

A shekarar 1982, ya kammala karatunsa na digiri na farko LL.B a jami’ar Ahmadu Bello na Zaria. Sai ya Kara gaba yayi Law school ta jihar legas a shekarar 1983.

Aikin Haruna Tsammani

Justice Haruna ya fara aiki ne a shekarar 1983, yayi aiki ne a matsayin lauyan gwamnatin jihar Bauchi a ministirin Sharia (Justice state ministry).

Sannan ya koma ministirin justice ta jihar gombe inda aka zabeshi a matsayin darakta na hukuncin jama’a(Public prosecution). Bayan kwazo da aiki ya taimaka masa wajen girma har ya kai da matsayin alkalin high court ta gombe ran 17 ga watan satumba 1998.

Ranar 16 ga watan juli na shekarar 2010, ya samu Karin girma zuwa Appeal Court inda yake cikin Alkali mutum biyar na kotun. Ya kasance yafi duka alkalai jimawa a aikin alkalanci a Appeal court.

Shafin Sadarwa Na Haruna Tsammani

Shafin Sadarwa Na Haruna Tsammani 
Shafin Sadarwa Na Haruna Tsammani

Alkalin ya kasance bayi account ko profile a kowacce manhajar shafin sadarwa, ya bar rayuwar gidansa da iyalensa a boye wa shafin sadarwa.

Iyalen Haruna Tsammani

Alkali Haruna yana da mata da yara, kuma musulmi ne wanda bai yarda da bayyana rayuwar sa wa mutane.

Arzikin Haruna Tsammani

Da yawan shekarun da yayi cikin aikin lauyanci da alkalanci na sharia ta najeriya, Justice Haruna Tsammani ya samu arziki kimanin miliyan dala $3.6m.

Hotunan Haruna Tsammani

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button