Cikakken Tarihin Umar Bago
Labaranyau.com ta kawo Muku tarihin Muhammad Umar Bago dalla dalla a sauwake kan rayuwarsa, Iyalansa, karatunsa, aikin sa da kuma siyasarsa.
Waye Umar Bago?
Honorable Muhammad Umar Bago gwamna ne a jihar Neja (Niger State), ya lashe zaben gwamna a zaben da ya gabata na shekarar 2023 a Jam’iyar APC. Tsohon Dan majalisan tarayya ne wanda yayi tenuwa uku shekara goma shaa biyu a majalisar yana wakiltar mutanen mazabar Chachanga na jihar Neja.
An haifeshi a minna babban birnin jihar Neja, Ranar 22 ga watan Fabrailu na shekarar 1974, Iyayensa Marigayi Alhaji Muhammadu Mustapha Barapen Nupe ya kasance dan fadar bida ne. Da mahaifiyarsa Marigayiya Hajiya Aisha Muhammad yar zuri’ar Jantabo ne na fadar Lapai. Iyayensa sun kasance qabilar Nupe.
Karatun Umar Bago
Ya Fara karatun sa na firamare ne a Marafa Primary School Minna, inda ya samu takardan gama Firamare FSLC a shekarar 1985, nan ya wuce ya cigaba da karatun sakandare a federal Government College Jos, nan ya samu takardan gama sakandare da Takardan WAEC a shekarar 1991.
Bago ya kammala digirin sa na farko a jami’ar Uthman Danfodio na Jihar sokoto inda ya karanta fasahar Siyasa (Political Science), yayi wasu karatun na gaban digiri wanda ake kira postgraduate degree daban daban wanda sun hada da Postgraduate Diploma in Management daga federal university of Technology Minna a shekarar 2001, yayi digiri ta Masters a fannin Kasuwanci fa gudanarwa Masters In Business Administration and Management In Economics a jami’ar Ambrose Ali da ke Ekpoma a shekarar 2003. Yayi wata Digiri ta biyu kuma a jami’ar Calabar da ke jihar cross rivers inda ya samu mAsters digiri a fannin kudade wato finance a shekarar 2005. Ya kasance dan jami’ar Cambridge ne na kasar burtaniya inda ya kammala a shekarar 2014.
Umar ya zama kwararre bayan samun horaswa kan gudanarwa a jami’ar London Graduate School a shekarar 2020 inda ya samu kwarewa kan Time Management. Ya kuma samu karramawa na Dakta (honoris causa) da kuma zama mamba na Mutane da siyasar Tattalin arziki (humanity and political economy) a jami’ar African school of diplomacy and international relations Abuja, jami’ar Estam kasar benin shekarar 2021.
Aikin Umar Bago Siyasa Da Kwadigo
Ya fara aiki ne a fannin banki ne inda ya girma yayin da ya taka matsayi da muqamai a aikin banki zuwa shekarar 2011 inda ya ajiye aikin. Sannan ya koma harkar siyasa. Ya shiga siyasa ne a lokacin da aka kafa jam’iyar CPC, inda ya lashe zaben majalisar tarayya a mazabar Chachanga.
Ya samu kware a aikin banki, bayan yayi aiki da manyan bankuna kamar su UBA, Standard Trust bank, FCMB, da kuma AfriBank. Ta inda ya samu horaswa da gogewa a wajen da kuma fitar da mafita kan har kar shugabanci.
A yau yana daga cikin masu ilimi a wurare daban daban kuma mai iya sarrafa magana a majalisar tarayya wanda najeriya ta samu tun bayan samun yan cin demokradiyya a shekarar 1999. Domin babu wata ministri ko hukumar dai taba ba domin fahimtar ayyukansu da gudanarwa Dan ayi gyara. Ya kawo sabbin dokoki da kuma korafi masu yawa Dan talaka ya mori Mulkin demokradiyya.
Siyasar Da Mukamai Umar Bago
Honarable Umar Bago ya fara aiki a matsayin sa dan majalisar tarayya ran 29 ga watan mayu shekarar 2011, bayan ya amshi kira daga mazabar sa domin wakiltarsu a majalisa da kuma cin zabe.
Ya Kara samun lashe zabe a karo na biyu a majalisar daga shekarar 2015 zuwa 2019. Haka kuwa ya Kara cin zabe a karo na uku a zaben 2019 saboda aminta da ya samu daga wajen mutanen sa.
Ya riqe mukamai a majalisar na duba kan gudanarwa a fannin banki da kudade, kasafin kudi, Ilimi, tsaron cikin gida najeriya, zantarwa bayani da fasaha(information, communication and technology). Wasu wuraren sun hada da Tsaro na kasa (defense), Aron kudi da basussuka, tsare tsaren kasa, cigaban tattalin arziki, Media, kungiyar ma’aikata, yansanda, da kuma asusun kasa.
A karo na biyu a majalisar, ya zama shugaban duba kan tsaro na ruwa da gudanarwa da ilimi, kuma mamba ne kan ayyuka, IDPs, jami’o’in ilimi, da kuma kwamitin ICT.
Haka a karo na uku da ya samu Komawa majalisar ya riqe ciyaman na kwamitin hadin kan Afirka, ya kuma zama mamban kwamitin Airforce, cin Hanci da rashawa, kasuwan kudi, kwadigo da aiki, zantarwa da lamuran jama’a, Shiga da fita na hanyar ruwa, Steel da Appropriation.
Mutum ne wanda yake son gaskiya da riko da gaskiya, dalilin haka ya samu goyon baya dan yin takarar matsayin shugaban majalisar tarayya da Shugaban majalisar Femi Gbajiabiamila inda ya zamo na biyu a zaben. Bago banufe ne wanda ya sanya idanunsa a gwamnan jihar neja kuma Allah ya bashi nasara a zaben 2023.
Aikin Alkhairi Na Umar Bago
A fannin taimako da jin kai, ba a bar Umar bago a baya ba, domin taimakawa mutanen sa. Ya kirkiro Bago foundation a shekarar 2010, wanda a shekarar 2020 ya Siya form din jamb wa yara 1000 dan shiga jami’ar domin samun ilimi. Ya kuma bada shinkafa trailer goma sha daya wa mutanen mazabar sa lokacin da aka fuskanci matsalar Covid 19. Yayi aikin hanyoyi masu yawa a Chachanga.
Wadannan abubuwan alkhairi da yayi yasa mutane suke kiransa da Mr empowerment wato mai dafawa mutane. Saboda ya tallafawa mutane dayawa da kuma kawo sauyin rayuwa a kowata fanni. Hakan yasa mutane barasu manta dashi ba.
Iyalen Muhammad Umar Bago
Honorable Bago yana da mata da yara guda uku.
Karramawan Umar Bago
Yasamu karramawa na mai jajircewa a majalisa Wanda yan jaridar majalisa ta bashi a ICC na birnin tarayya a shekarar 2021
Karramawa na mulki na adalci wanda Nigeria vanguard for equity a shekarar 2021
Dan majalisan tarayya na shekara na Democracy Heroes a transcorp hilton a shekarar 2019
Karramawa na girma wanda Riyadul Quran islamic foundation na fadar Suleja