Biography

Cikakken Tarihin Babagana Zulum, Karatunsa, Aikinsa, Siyasarsa, Iyalensa

Cikakken Tarihin Babagana Zulum

Labaranyau.com ta kawo takaicaccen bayani da tarihi siyasa, Aiki, iyali da karatun Babagana Zulum a saukake.

Babagana Umara Zulum Malamin Jami’a ne kuma dan siyasa, Wanda aka haifa ranar 26 ga watan augusta ta shekarar 1969 a jihar Borno, kauyen zulum na karamar hukumar Mafa.

Cikakken Tarihin Babagana Zulum 
Cikakken Tarihin Babagana Zulum

Karatun Babagana Zulum

Zulum yayi karatun firamare a Mafa primary school daga shekarar 1975 zuwa 1980.

Ya wuce karatun sakandare a gwamman sakandare Munguno daga shekarar 1980 zuwa 1985. Ya shiga Ramat polytechnic maiduguri inda ya samu takardan diploma, inda ya karanci injiyar noman rani a shekarar 1998, kuma a shekarar 1990 zuwa 1994 baya ya karanci injiniyar noma a jami’ar maiduguri inda yayi digirinsa ta farko.

Bayannan yayi bautar kasa a polytechnic na jihar katsina. Nan ya wuce jami’ar Ibadan inda yayi digiri ta biyu masters a fannin kimiyar noma a shekarar 1997 ya kammala a shekarar 1998. Zulum bai huta ba ya wuce karatun digirin digirgir a kan kimiyar ruwa da kasa  daga shekarar 2005 zuwa 2009.

Aikin Babagana Zulum

Aikin Babagana Zulum
Aikin Babagana Zulum

Babagana Zulum ya fara aiki ya fara aiki da gwamnatin jihar borno, ministirin noma a matsayin Asistant Technical officer a shekarar 1989, a shekarar 1990 ya koma unified local government service a matsayin senior field overseer har ya kai matsayin principal injiniyar ruwa.

A shekarar 2000 ya zama mataimakin malamin jami’a na jami’ar maiduguri a nan ya kai matsayin farfesa, Zulum ya riqe muqamai daban daban kamar su mataimakin dean, mai riqon kwaryar dean da kuma dean a faculty na kimiya (engineering) daga shekarar 2010 zuwa 2011.

A shekarar 2011, an zabe Babagana a matsayin Rector na Ramat polytechnic duk da muqamin ya cigaba da koyarwa a jami’ar Maiduguri.

Siyasar Babagana Zulum

Siyasar Babagana Zulum
Siyasar Babagana Zulum

Tsohon gwamnan Borno sanata Kashim Shettima ya bawa Zulum  muqamin kwamishinar reconstruction, rehabilitation da resettlement na jihar Borno matsayin da ya riqe daga shekarar 2015 zuwa 2018.

Yayi Takarar Gwamna a jihar Borno ya kuma lashe zaben na shekarar 2019. Ranar 9 ga watan Maris ya ci zabe da kuri’a 1,175,440 inda ya doke dan jam’iyar PDP Muhammad Imam wanda ya samu kuri’u 66,115.

Hukumar zabe ta Inec tayi rajistar masu zabe 2,316,218 a jihar, wanda 1,292,138 ne aka tantance domin zabe. Ya fara aiki a matsayin sa na zababban gwamna ran 29 ga watan mayu shekarar 2019.

A shekarar 2023 ya karayin takara gwamna a borno a jam’iyar APC inda ya Kara lashe zaben, Yanzu haka gwamna ne mai ci.

Kasashen Da Zulum Ya Ziyarta

Kasashen Da Zulum Ya Ziyarta 
Kasashen Da Zulum Ya Ziyarta

America, Dubai, Canada, Spain, China, Saudi Arabia, Pakistan, Niger, India, Turkey, Zambia, Uganda, Tanzania, Ghana, Burkina faso, Mali da sauransu.

Iyalen Babagana Zulum

Iyalen Babagana Zulum
Iyalen Babagana Zulum

Zulum bai bayyana komai kan iyalensa ba, Amma Yana da aure da kuma yara.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button