Biography

Cikakken Tarihin Nasiru Ahmed El-Rufai, Karatun, Iyalen, Sana’arsa, Siyasarsa, Karramawarsa

Cikakken Tarihin Nasiru Ahmed El-Rufai

Nasir Ahmad El-Rufai an haifeshi ranar 16 ga watan fabrailu shekarar 1960 a Daudawa jihar katsina najeriya. Dan siyasa ne wanda yayi gwamna na shekara takwas a jihar kaduna daga 2015 zuwa 2023. Yayi ministan birnin tarayya daga 2003 zuwa 2007, ya rike darakta ta bureau of public service. Yana daga cikin mambobin da suka samo jam’iyar APC.

Iyalen El-Rufai

An haifi El-rufai daga cikin qabilar fulani na Daudawa, mahaifinshi ya rasu yana mai shekara 8, ya samu kula wajen bappan shi a kaduna. malam yana da mata uku sun hada da Hadiza Ismail uwar gida kuma marubuciya kuma mawallafiya wanda ke gudanar da Gidauniyar Yesmin Elrufai, sunan yar malam nasiru da ta rasu a 2011, akwai Asiya da kuma Ummi.

DOWNLOAD MP3

Nasiru El-rufai Yana da yara wanda sun hada da Muhammad Bello El-rufai ya kasance dan majalisar tarayya daga mazabar tarayya kaduna ta arewa a jihar kaduna. Bashir, Hamza, Mustapha, bilkis yasmin da sauransu.

Karatun Nasiru El-Rufai

Karatun Nasiru El-Rufai 
Karatun Nasiru El-Rufai

Malam nasiru ya samu ilimin boko a kaduna, yayi karatun sakandare a barewa Kwalaji na Zaria. Tsohon shugaban kasa Umaru Yaradua shine shugan dakin kwanan su ta makaranta a lokacin. A shekarar 1979, ya gama gwarzon shekara inda ya samu karramawa da Academic Achievement daga wajen Barewa Old boys.

Malam yayi digirinsa ta farko a jami’ar Ahmadu Bello a zaria inda ya karanci quantity survey ya gama da first class. A shekarar 1984 ya kammala masters a business Administration daga jami’ar Ahmadu Bello. Yayi karatun gaba a jami’o’i  daban daban wanda sun hada da Georgetown school of foreign service ta jami’ar Georgetown a Washington DC inda ya samu Horaswa kan shugabanci da privatization.

DOWNLOAD ZIP

A shekarar 2008 ya kammala digiri a harkan sharia wato Law a jami’ar landan. Ya kuma yi Masters kan gudanarwa ta jama’a Public Administration daga John F Kennedy Makarantar Gwamnati ta jami’ar Harvard a 2009. Ya samu satifiket na Dokar jama’a Public policy and management ta Edward A Mason fellow daga shekarar 2008 zuwa 2009.

Ya koma digirin digirgir a shekarar 2017 karanta harkan gudanarwan gwamnati da kuma duba cikin dokoki a jami’ar Majalisan dinkin duniya Netherlands.

Sana’ar Elrufai

Sana’ar Elrufai 
Sana’ar Elrufai

Malam ya bude kampani mai suna El-rufai and Partners na quantity survey wanda ya yi aiki da mutane uku a shekarar 1982 zuwa 1998. A mulkin soji a shekarar 1983 zuwa 1998, sun samu kwantiragin gine gine lokacin da ake gina birnin tarayya. Inda shi da abokan aikin sa suka zama kananan miloniya.  Duk da aikinsa da yakeyi Nasiru ya rike mukaman gudarwa na manyan kampanin waya na kasar waje AT&T Network Systems International BV da Motorola Inc.

Siyasar Elrufai

Siyasar Elrufai 
Siyasar Elrufai

Bayan mutuwan Tsohon shugaban kasar Najeriya Sani Abacha, Janar Abdulsalami Abubakar ya zabe shi mai bada shawara kan tattalin Arziki, anan yayi aiki da bankin duniya da IMF.

Bayan Zabe a shekarar 1999, shugaban kasa na mulkin demokradiyya Olusegun Obasanjo ya bashi darakta na Bureau of Public Enterprise da kuma sakataren National council of privatization inda ya jagoranci siyar da kampanonin kasar tare da mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Shekarar 2003, Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zabi malam a matsayin ministan birnin tarayya. A wannan lokacin malam nasiru ya gigita birnin tarayya da gyara manya manya. Domin a dawo abi tsarin yadda aka zana garin Abuja kasancewar ta fadar shugaban kasa. Ya kirkiro Abuja Geographic information system ta inda Abuja ta zama jaha ta farko ta zanenta ke yanar gizo tare da rajista.

Tare da shugaban kasa da mambobi kan gudanar da tattalin arziki, ya jagoranci kawo canji a ma’aikatu na kasa su zama sun aikatu bayan rashin aiki a mulkin soji. Bayan muqamin shi na minista ya riki kwaryar ministan kasuwanci so biyu da ministan tsaron cikin gida.

Elrufai ya jagoranci kwamitin da suka kawo mortgage system da national IDcard system da karin wutan lantarki da kuma siyar da gidajen da gwamnatin tarayya ta Gina a Abuja. Kusan karshen mulkin Obasanjo, Nuhu Ribadu yace Elrufai shi ne mutum na biyu a kasar. Musamman bayan matsala da aka samu tsakanin Obasanjo da Atiku.Saboda yarda da Obasanjo ya baiwa Malam Nasiru hakan ya fusatar da yan siyasa dayawa.

A shekarar 2008, Malam ya tafi buya inda ya ke sukan gwamnatin Yaradua, a shekarar 2010 ya dawo najeriya inda EFCC hukumar cin hanci da rashawa suka kama shi, ya kuma amsa tambayoyi ya goge batancin suna da akayi mai. A shekarar 2011 ya shiga jam’iyar CPC tare da Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya bayyana kudirin takarar gwamna a shekarar 2014. Inda ya lashe zaben gwamna a jihar kaduna a jam’iyar APC da kuriu sama da miliyan daya inda ya doke gwamna mai ci Mukhtar Ramalan.

A shekarar 2019 ya Kara takara ya lashe zaben inda ya doke Ashiru kudan na PDP da tazarar 200,000.

Ran 29 ga watan mayu na shekarar 2015, an rantsar da Malam a matsayin sa na gwamna na 22 a jihar kaduna. A jawabin sa na ranar rantsar wa, ya bayyana cewa shi da mataimakin sa zasu rage albashinsu kashi biyu suna karban rabi saboda halin da ake ciki na tattalin arziki. Ran 6 ga watan augusta 2015 a cikin ayyukansa na farko ya saka an kulle asusun gwamnati guda 470 na ministiri daban daban, Aka hada a asusu guda na gwamnati wanda hakan kudi Biliyan 24.7 ya koma asusun jiha ta CBN.

Bayan kulle asusun hakan yasa an toshe wasu gurbin da ke yoyo ya kuma rage badakala na kudin gwamnati. Dokar asusu daya na gwamnati ya saka an samu raran kudi naira biliyan 1.2. Malam Nasiru ya kawo canji a aikin gwamnati ta hanyar rage ministiri 19 zuwa 13, ya kuma rage famanet sakatare daga 35 zuwa 18. Duk dai dan a rage tsadan gudanar wa na gwamnati.

Elrufai ya zabi kwamishinoni 13, masu bashi shawara 10, masu taimaka mishi guda 12 wanda suke a maimakon kwamishina 24.  Special advisers guda 41 da special assistant guda 400.

A matsayin sa na gwamna ya kawo a harkan ilimi inda ya kori maluma 22,000 wanda basu cancanta ba ya kuma kawo dokar ciyar da dalibai miliyan daya da Rahina basu abinci so daya a rana a firamare na gwamnati. Wanda hakan ya rage wa iyaye kashe naira biliyan uku. Ya kuma soke karban kudin makaranta da wasu kananan kudade da ake karba a hannun dalibai na firamare da junior sakandare.

Ran 28 ga watan maris shekarar 2020, an samu Malam Nasiru da cutar Covid-19, hakan ya biyo da daukan mataimakin saka dokar ba fita dan dakile yaduwar cutar.

Elrufai ya saka an yan firsuna mutum 12 a kaduna, 10 ciki sun kusa kare kwanakin su a fursuna wasu kuma Saboda girma. Ya rage wa mutum daya hukuncin kisa zuwa zama a fursuna har tsawon rayuwar sa. Ran 1 ga watan augusta 2023, ya samu tantancewa a Majalisan dattawa bayan zaben shi da shugaban kasa bola tinubu yayi a matsayin minista a gwamnatin sa, Amma bayan korafe korafe da akayi daga mutane zuwa kungiyoyi irinsu CAN da yan kudancin kaduna ta nuna zahiri cewa hassada ta qabilanci da banbanci addini yasa akayi korafi hakan yasa shi janye wa duk da an bi kafa ya dawo bai dawo wa. Nasiru Elrufai ya samu sarautar Gbobaniyi na kasar Ijebu wanda mai martaba Oba sikiru kayode Adetona, Ogbagba II ranar Asabar 16 ga watan Disamba shekarar 2023.

Karramawar Elrufai

Karramawar Elrufai 
Karramawar Elrufai

A watan oktoba na shekarar 2022, Shugaban kasar najeriya  ya karrama malam nasiru da CON  ta kasa (commander of the order of Niger).

Hotunan Elrufai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button