Biography

Cikakken Tarihin Sadiya Umar Farouk, Karatunta, Aikinta, Siyasarta, Iyalenta, Hotunan

Cikakken Tarihin Sadiya Umar Farouk

Sadiya Umar Farouk wanda aka haife ta a ranar 5 ga watan Nuwamba a shekara ta alif dari tara da saba in da hudu (1974), ta kansance yar siyasa ne a najeriya kuma ita ce ministar harkokin agaji da jin kai a mulkin Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari , domin kula da musiba, jin kai na gaggawa da kuma ci gaban al’umma a Najeriya.

Karatun Sadiya Umar Farouk

Tsohuwar ministan jin kai da dauki na gaggawa domin cigaban yan najeriya Hajiya Sadiya tayi karatu kuma ta samu ilimi na boko a makarantar sakandaren mata na gwamnati tarayya FGGC gusau na jihar zamfara, ta kuma yi karatun jami’a  a jami’ar Ahmadu Bello a garin Zaria na jihar kaduna inda ta samu takardan digiri a fannin kasuwanci a shekarar Alif dubu daya da dari tara da casain da takwas 1998.

Ta samu digiri na biyu a fannin kasashen waje da kuma diflomasiya a shekarar Dubu biyu da takwas 2008, ta kuma karayin digiri na biyu a fannin kasuwanci a jami’ar Ahmadu Bello zaria a shekarar dubu biyu da sha daya 2011.

Aikin Sadiya Umar Farouk

Sadiya tayi aiki da Majalisan tarayya daga shekarar 1999 zuwa 2000 inda tayi aiki a kwamitin Safaran jiragen sama da kuma kasafin kudi na majalisan dattawa.

Tayi aiki da kampani mai zaman kansa na tafiye tafiye Pinnacle travel and tours daga shekarar 2001 zuwa 2003. Sannan tayi aiki da hukumar dokokin tarayya a matsayin jami’ar gwamnati har zuwa shekarar 2010 inda ta koma tafiyar siyasa.

Siyasar Sadiya Umar Farouk

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bawa Sadiya Umar Farouk matsayin ministan jin kai da dauki na gaggawa a mulkin sa a watan Yuli na shekarar Dubu biyu da sha tara 2019. Ta kasance mai karamin shekaru cikin sauran ministocin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Alaqar ta da Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kullu ne da kuma samo asali tun takarar sa inda tayi jagora a wani sashe na tafiyar a lokacin da ya fito neman kujerar shugaban kasa a tsohuwar jam’iyar congress for progressive change. Ta rike mukamin ma’ajiyar Kudi na jam’iyar CPC na kasa kuma ta kara zama ma’ajin jam’iyar APC daga baya.

A shekara ta Dubu biyu da sha tara na 2019, ofishin shugaban kasa ta tuhumi ministan jin kai da dauki na gaggawa Sadiya don yin amfani da karfin da ya wuce ikon matsayinta na aiki ta hanyar daukar karin mataimaka da ma’aikata fiye da yadda hukuma da kundin tsarin kasa ta tanada ta kuma amince da shi da kuma jinkirta kudaden jin kai na wata-wata na masu aiki da kuma tallafi na N-Power, shirin tsoma bakin jama’a na gwamnatin tarayya. Bikin auren Sadiya da Sadique Abubakar Tsohon Shugaban Sojan Sama, Ministan Jin kai ta kashe kudade sosai a lokacin bikin Aure  wanda ya dade yana zuwa majiyoyin dangi bayan zargin aure da akayi tsakanin ta da Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Duk da kalubalen kasafin kudin da kasa Najeriya ke fuskanta tare da karancin kudaden shiga, Ana zargin ta fitar da kudade bila adadin yayin da ake fuskantar dumbin matsaloli da manufofin yakin neman zabe, da kuma dakile kudaden  aiwatar da ayyukan Covid-19.

Iyalen Sadiya Umar Farouk

Shafin labaranyau.com tana kan bincike don samo bayani kan iyalen tsohuwar ministan, Amma tana da aure ta auri Tsohon shugaban sojin sama na kasa Airmarshal Saddique Abubakar wanda yayi takarar gwamna a jihar Bauchi a shekarar 2023 a jam’iyar APC.

Hotunan Sadiya Umar Farouk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button