Biography

Cikakken Tarihin Beta Edu, Rayuwarta, Karatunta, Iyalanta, Aikinta, Karramawarta, Hotunanta

Cikakken Tarihin Beta Edu 

Beta Edu wanda aka haifa a shekarar Alif dubu daya da dari tara tamanin da shida 1986 ranar  27 ga watan Oktoba. Ta kasance yar Siyasar najeriya wanda aka dakatar da ita a matsayin ta na ministan jin kai da tallafi wa jama’an najeriya bayan zargin canza wa kudi Naira miliyan dari biyar da tamanin da biyar na kudin gwamnatin tarayya zuwa asusun mutum daya.

Edu ta rike matsayin shugaban mata na jam’iyar APC, kuma tayi kwamishinan lafiya zuwa shekarar 2022 inda ta ajiye aikin. Tayi Shugabancin kwamishinonin lafiya na kasa.

Rayuwar Beta Edu

Beta wanda aka haifa a jihar lagos, mahaifin ta shine Emmanuel Eke wanda ya kasance dan kasuwa ne kuma yayi aiki da kampanin Injiniya, mahaifiyar ta ta kasance uwa ce a gida. Tana da yan uwa ciki daya guda gudu wanda daya daga ciki tagwayen ta ne.

Mahaifinta asalin sa dan Umunze na jihar Anambra kuma mahaifiyar ta yar Yala na jihar Cross River.

Karatun Beta Edu

Edu ta kammala karatun sakandaren ta a shekarar dubu biyu da daya 2001, a makarantar gwamnatin tarayya na mata a garin calabar, nan tayi gaba domin karatun digiri na farko a fannin likitanci a jami’ar Calabar a shekarar 2009.

Ta samu takardan diplomar sama da digiri a fannin lafiyar Al’ummar kasashen da ke kokarin cigaba (PGD in Public Health in developing countries) daga London school of hygiene and tropical. Tayi digiri na biyu shima a wannan jami’ar London tayi akan public health kuma tayi digirin digirgir a fannin Public health a jami’ar Texila American.

Iyalen Beta Edu

Beta Edu ta auri wani daga karamar hukumar Abi a jihar cross river. A Yanzu bata da aure Amma tana amfani da sunan Tsohon mijinta Edu wanda suke da yara uku tare.

Aikin Beta Edu

A shekarar 2015, Edu ta zama mai karancin shekaru wanda gwamnan Cross river Benedict Ayade ya nada a matsayin masu bada shawara a fannin kananan Asibitin unguwanni. A shekarar 2020 ya zama ciyaman na kwamitin Ibtila’in cutar Covid 19 a jihar cross river.

A watan augusta ne na shekarar 2020 ta zama zababbiyar ciyaman na kwamishinan lafiya ta kasa.  Ta zama fellow na royal school of public health da kuma African institute of public health professionals.

Beta ta zama shugaban mata mai karamin shekaru na jam’iyar APC a watan maris Shekarar 2022.

A matsayin ta na shugaban mata na jam’iyar APC a zaben shugaban kasa da ta gabata na shekarar 2023 ta tabbatar wa mata samun kaso 35 a gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.

A watan Juli na shekarar 2023, Shugabannin mata na jihohi 36 na jam’iyar APC  harda na birnin tarayya Abuja sun bada lambar yabo a kan Beta Edu, sunyi hakan ne yayin da suka ziyar ce shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a fadar shugaban kasa na villa Abuja.

Gwamnatin tarayya ta hanun hukumar cigaban mata na Maryam Babangida ta jagorancin Darakta Janar Asabe Vilita Bashir da hadakayyar ministirin mu’amalar mata da cigaban al’umma, sun karramawa beta Edu da Award of excellence in leadership for gender inclusion and women Empowerment. Bayan bayyana hazaka da jajircewa kan tallafi wa mata da kuma aiki tukuru domin tallafawa yara da marasa karfi a najeriya.

Watan yuli na shekarar 2023, Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya zabe ta a matsayin minista inda ya tura sunan ta cikin ministoti 28 domin tantancewa. Wanda yazo cikin tarihi cewa ita ce mace minista ta farko daga jihar cross river kuma mai karamin shekaru a republic ta hudu.

A watan augusta na shekarar 2023, aka rantsar da ministan jin kai da tallafi na gaggawa, Sannan aka canza ta a matsayin shugaban mata na jam’iyar APC na kasa.

Karramawar Beta Edu

Shekarar 2020 ministirin mata na tarayya ta karrama ta da Nigeria Quintessential Woman Award.

Hukumar bautar kasa ta kasa a shekarar 2020 ta karrama ta da Award of Excellence.

Ta samu Karramawar Medical Expert of the Year na shekarar 2020.

Ministirin mata na tarayya ta karrama ta da Award of excellence in Gender inclusion a shekarar 2023.

Hotunan Beta Edu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button