NEWS

Ayyukan Alheri Da Tsohon Darakta Janar NTA Yakubu Ibn Muhammed Yayi Wa Talakawa A Jos

Ayyukan Alheri Da Tsohon Darakta Janar NTA Yakubu Ibn Muhammed Yayi Wa Talakawa A Jos

Hukumar makarantar Asasu-Sunnah Private School Anglo-Jos tana miƙa saƙon godiya da jinjina ta musamman ga tsohon Babban Daraktan tashar talabijin ta ƙasa (NTA) Malam Yakubu Ibn Mohammed, bisa gudunmawar ya bayar kuma yake cigaba da bayarwa ga al’amuran da suka shafi tafiyar da harkokin wannan makaranta, na baya bayan nan shi ne tallafin da ya bayar a bikin yayen daliɓan aka gudanar ranar 27-08-2023, karo na 8. Duk da wannan gagarumar gudunmawa da tsohon Babban Daraktan kuma Tafidan Jos ya bayar gudunmawa a wajen bikin yayen ɗaliban, bai hana shi taimakawa maɓukata da ke cikin anguwar da maƙwaftansu, domin sauƙaƙa musu halin rayuwar da ake ciki.

Malam Yakubu Ibn Mohammed, wanda kuma shi ne Tafidan Jos, ya jima yana mazauna wannan unguwa, musamman yaran talakawa waɗanda yake biyawa kuɗin makaranta, tare da tausayawa gajiyayu da nakasassu dake Anglo Jos.

DOWNLOAD HERE

Har wa yau Tafidan Jos ya kasance mutum ne mai daraja da ƙima a idanun al’umma, ga shi da tausayi da adalci. Ba ya wulaƙanta mutane, kuma kowa nasa ne. A kullum bashi da burin da ya wuce ya ga ya kyautatawa talakawa.

Kodayake an ce, ba komai ba ne ake ambatawa na alherin da mutum ya yi, saboda wasu abubuwan tsakanin bawa ne da Ubangijinsa. Amma wasu ayyukan ya zama dole mu faɗa saboda wasu ma su yi koyi da shi!

A azumin da ya gabatar, wannan bawan Allah, Tafidan Jos, ya ɗauki nauyin abincin mutane sama da 400 yana ciyar da su, domin sauƙaƙa wa al’umma a lokacin tsanani na rashin kuɗi a garin Anglo Jos.

DOWNLOAD MP3 HERE

Yakubu Ibn Muhammed
Yakubu Ibn Muhammed

Bayan haka, wannan jagoran bai tsaya haka ba lura da yadda rayuwa ta yi tsada ya ƙara zaƙulo iyayenmu guda biyar ya musu albashi, domin sauƙaƙa mu da iyalansu a kowanne wata.

Wannan shi ne dalilin da ya sa muka ce ya zama dole mu yabawa jagoran talakawa kuma Tafidan Jos, bisa gudunmawar da yake bayarwa a wannan unguwa tamu da ma ƙasa gaba ɗaya.

A madadin shugabannin wannan makaranta muna ƙara miƙa saƙon godiyar mu ta musamman ga wannan jajirtaccen bawan Allah, ɗan kishin ƙasa, mai tausayin talakawa. baya mai goya marayu. Yallaɓai, muna yi maka fatan alheri duniya da lahira. Muna roƙon Ubangiji Ya maka kariya daga dukkanin sharri ya talafa maka a wannan aikin alheri, ya kuma sa sauran jama’a masu dama irin taka su yi koyi da kai.

Yakubu Ibn Muhammed
Yakubu Ibn Muhammed

Sa Hannun Sakataren Makaranta Asasus-Sunnah Private School Jos,
A madadin shugabannin gudanarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button