Labaran Yau

Babban Hotel A Duk Duniya Cikin Saudi Arabia [Abraj Kudai Photos]

Abraj Kudai Shine Hotel Mafi Girma A Duniya Yanzu Hake, Abraj Kudai hotel ne da aka gina a Kingdom of Saudi Arabia, Middle East.

Daga farko anso bude hotel dinne a shekarar 2017, amma aka dakatar da ginin a shekarar 2015 saboda matsalolin kudi.

A binciken manema Labaranyau har a yanzu tsakiyar 2024 ba a buɗe hotel ɗin ga jama’a ba, anakan kawata hotel din da ababen duniya da more rayuwa.

Idan aka kammala shi, zai kasance daya daga cikin manyan hotel a duniya, wanda ya kunshi zobe na hasumiya 12 masu tsayin benaye 45.

Abraj Kudai 100 Rooms
Abraj Kudai Hotel

Hotel din nada matukar girma akwai dakuna 10,000, gidajen abinci 70, da kuma jirage masu saukar ungulu guda hudu.

Haka kuma za a yi benaye guda biyar don amfani da gidan sarautar Saudiyya kadai.

A cewar Arab Business, 10 daga cikin hasumiyai za su samar da masaukin taurari hudu, yayin da sauran hasumiyai biyu za a kebe su don abokan ciniki na musamman da ke ba da abubuwan more rayuwa wa masu kudi.

Ga hotunan Hotel Din Daga Bisani  ⇓

 

Ga Bidiyon Cikin Abraj Kabai Daga Bisani ⇓

 

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button