Labaran YauNEWS

Bani Da Zabi A Zaben 2023 – Buhari

Bani Da Zabi A Zaben 2023 – Buhari

A daidai lokacin da kakar babban zaben shekarar 2023 a Nijeriya ke kara karato wa, Shugaba Muhammadu Buhari ya sake yin magana kan magajin buzun Karagarsa.

A kwankin baya cikin wani shirin talabijin an jiyo shugaba Buharin na furata cewa, ya na wanda yake son ya dare Karagarsa, amma bai kai ga bayyana sunan wanda zai gaje shinba don gudun kar a farwa wanda zai gaje shin.

Buhari, ya sake maimaita maganar a jiya Litinin bayan an sauko daga Sallar Idin karamar sallah ta bana da aka gudanar a Barikin Mambilla da ke Abuja, inda ya kara jaddada kudurinsa na ganin an gudanar da tsaftatancen zabe a 2023.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Shugaban ya kuma umarci shugabannin rundunar tsaron soji da sauran jami’an tsaro da su yi dukkan mai yuwa don don fatattakar ‘yan ta’adda da kuma kawo karshensu.

Aikinsu ne su gano malafar ‘yan ta’adda tare da kawo karshensu, zamu ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin daukcin ‘yan Nijeriya, musamman saboda manoma su koma gona su ci gaba da noma don a wadata kasa da abinci “. In ji Shugaba Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button