Girke GirkeLabaran Hausa

Yadda Ake Sarrafa Funkaso

Ita Funkaso abu ne mai dadi da saukin sarrafa wa amma dayawan mutane sukan gagara hadawa yayi dadi sosai.

Domin koyan yanda ake sarrafa Funkaso biyomu kadan dan ganin yadda muke sarrafa funkaso.

Abubuwan Hada Sarrafa Funkaso

1. Fulawa

2. Yeast

3. Gishiri

4. Man gyada

Yadda Ake Hada Sarrafa Funkaso

  • Dafarko zaki tankade fulawarki ki sa gishiri kadan sai ki ajiye a gefe.
  • Dauko yeast asa masa ruwan dumi ba me zafi ba da suga karamin cokali daya a juya.
  • Sai a rufe ki ajiye a gefe kamar na tsawon minti biyar.
  • Idan ya na da kyau za’aga ya yi kumfa ya kumbura amfanin yin hakan don a san yeast din mai kyau ne.
  • Sai a juye yeast din cikin filawan adan kara ruwa a kwaba shi kamar kwabin fanke
  • Sai a rufe a kai rana saboda tashi kamar minti 20-30 idan ya taso sai a kara buga shi sosai a ajiye a gefe.
  • Dauko kasko a daura kan wuta, a zuba man gyada idan ya yi zafi, sai a na diban kwabin funkasau din kadan kadan ana fadada shi da hannu ana sawa a mai ana soyawa har sai ya soyu, sai ki tsame da matsami.

Ana iya cin funkasau da miyan stew, miyan taushe, Ko miyar ganye.

A ci dadi lafiya.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button