
Yadda ake Miyan Romo
Ita Miyar romo miyace wanda ake ci da tuwon sakwara ko na Shinkafa mafi yawan lokuta. Miyan ta kasance cikin miya masu Dadi sosai a kasar hausa da kewaye.
Biyoni kadan dan koyar yadda ake girka miyar romo cikin sauki batareda bata lokaci bah.
Kayan hadi
1. Namar rago mai kashi
2. Attaruhu
3. Tattasai
4. Albasa
5. Tumatur
6. Chitta
7. Tafarnuwa
8. Masoro
9. Maggie
10. Gishiri
11. Mangyada
12. Ganyan albasa
Yadda Ake Hada Miyan Rama
- Da farkon za’a wanke namar ragon sai a daka citta, tafarnuwa, masoro a zuba a kai.
- A zuba Maggie da gishiri da albasa sai a daura a kan wuta,
- Idan ya fara kamshi sai a wanke kayan miya a markada yayyi laushi aman tumatur din kadan ne bai fi kamar guda biyar ba,
- A zuba a ciki a rufe ya cigaba da dafuwa za a bar shi yayi ta dafuwa ne har sai Naman ya bar jikin kashin
- Sai a wanke ganyen albasa a yanka a zuba sai a barshi ya cigaba da nuna sai a sauke.
- Kamin nan tuwon mu ya kammala, Sai a zuba a faranti ko kwano dan jindadin miyar romo.
- Ana cin shi ne da tuwon sakwara ko semovita.