
Yayin da jihar Bauchi ta sake mallakar kamfanin Steyr
Gwamnatin jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Sanata Bala Abdukadir ta sake mallakar gawurtaccen kamfanin ƙere-ƙeren nan da aka fi sani da Styer, cikin shirin ta na farfaɗo da masana’antu a wani matakin samar da ayyukan yi da kuma yaƙi da zaman kashe wando.
Da yake jawabi cikin wani kwarya-kwaryar taro a fadar gwamnati, Gwamna Bala ya bayyana masana’antar a matsayin ɗaya daga cikin wuraren cin abinci ga dubban yan jihar Bauchi amma aka yi watsi da ita, kana ya yabawa Bankin Kasuwanci da kuma gwamnatin tarayya kan bada haɗin kai don nasarar shirin.
Ya ƙara da cewa gwamnatin sa ta ware sama da naira biliyan ɗaya da rabi don biyan basuka da Bankin Kasuwanci kafin sake mallakar masana’antar.
Mohammed ya ƙara cewa an kuma biyan naira miliyan ɗari shida da goma sha biyar don biyan tsoffin ma’aikatan kamfanin a watan gobe.
Daga yanzu, a cewar Gwamna Bala, gwamnatin sa ta dukufa wajen inganta masana’antu da sana’o’in tafi-da-gidan ka, sanya hannun jari a harkar noma, motoci masu amfani da iskar gas, masu amfani da lantarki da kuma hasken rana don inganta tattalin arziki, kana ya ja kunnen masu baba-kere da filaye.
Shugaban kwamitin karɓa da miƙa masana’antar kuma kwamishinan ayyuka na musamman Faruk Mustapha yabawa hangen nesan gwamnan yayi kana yace yayin da ake dab da kammala yarjejeniyar musayar bayanai da takardu, ana kuma shirye-shiryen fara aiki da shi.
Ga Hotuna
Discover more from Labaran Yau
Subscribe to get the latest posts sent to your email.