Biography

Cikakken Tarihin Qing Madi, Rayuwanta, Sana’arta, Wakanta, Arzikinta, Wakokinta

Cikakken Tarihin Qing Madi

Labaranyau.com tazo da tarihin Qing madi, da kuma cikakken bayani ga me da rayuwarta, karatunta, wakokin ta da sauransu.

Qing Madi wanda aka fi sani da D Glitch, ta kasance mawakiya kuma marubuciyar waka daga najeriya wanda ke samun shahara a Yanzu. Ta fara samun hankalin mutane a kan ta bayan ta sake wakar ta mai taken See finish.

Cikakken Tarihin Qing Madi
Cikakken Tarihin Qing Madi

Rayuwa Da Sana’ar Wakan Qing Madi

Ita chukuma ta tashi tare da yan uwanta a hannun uwarsu. Ta fara acting tun tana yar karamar yarinya sosai a in da take shiga gasar basirar wasannin kwaikwayo a makaranta da kuma waka data keyi a tare da manya a coci.

DOWNLOAD MP3

See finish ya kasance wakar ta da ya shahara a duniyan waka wanda ta sake a shekarar 2022 kuma ya samu daukaka a Shafin sadarwa ta TikTok. Ta saki waka guda uku a shekarar 2023 hakan ya zama dalilin da yasa mutane ke Kara sanin ta da kuma sanuwa cikin kasuwar waka bayan concert din da tayi a legas najeriya a event mai taken homecoming Event. Fannin wakar ta ya Hada da R&B, Pop, Soul, da kuma afrobeat.

Manhajar waka ta Spotify sun bayyana cewa sun zabe ta Qing Madi ta zamo madubin su a watan Yuni na shekarar 2023. Na sanya ta ambasada na Spotify Africa.

DOWNLOAD ZIP

Wakar Qing Madi Ole wanda tayi da Bnxn ta saka ran 21 ga watan juli shekarar 2023. Wakar ta samu shahara a jadawalin Apple Music.  Ya kuma haura a jadawalin wakoki dari na najeriya wanda ya so a na 12. Wakar ta shiga jadawalin Afrobeat inda ta samu matsaya a na 16.

Sana’ar Wakar Qing Madi

Sana’ar Wakar Qing Madi
Sana’ar Wakar Qing Madi

Wakar Qing see finish ta samu kunnuwan sauraro dubunnai a manhajar wakoki harda AppleMusic inda ta kai matsayin na 87 cikin dari wakoki masu tashe a najeriya.

See finish waka ce wanda aka sake ran 14 ga watan Oktoba 2022, a manhajar Audiomack wanda Ramoni ya shirya, zuwa yanzu ta samu yawan jin wakar sama da 600,000 a manhajar wakoki.

Zamu iya cewa muna zaton zata iya girma ta shahara sosai nan gaba Saboda Yadda ta bayyana shigar ta waka Yadda tayi performance a legas.

Arzikin Qing Madi

Arzikin Qing Madi 
Arzikin Qing Madi

An qayyade cewa tana da dala dubu hamsin Saboda tana samun kudade ta performance.

Wakokin Qing Madi

Wakokin Qing Madi
Wakokin Qing Madi
  1. See finish
  2. See finish (speed up)
  3. See finish featuring Lyrical saike

Karatun Qing Madi

Karatun Qing Madi
Karatun Qing Madi

Qing Madi tayi karatun ta ne a babban birnin Jihar Edo, Benin city. Ta kammala karatun sakandaren ta ne a Negbenebor International School.

@qingmadi1

♬ See Finish (Sped Up) – Qing Madi

Qing Madi Yar Najeriya Ce?

An haifi Qing a benin city dake jihar Edo.

Tattaunawar Da Akayi Da Qing Madi

Yar shekara 16 tayi hirar rayuwanta da kuma bayani Akan Sana’ar ta na waka tare da Guardian Life, inda ta bayyana musu Yadda ta samu cigaba a harkan waka.

Ki Fada mana Yadda kika samu sunanki na waka:

Qing Madi: Qing suna ne da na samo shi a tafarkin yancin mata (feminism). Qing mace ce mai yanci kuma bata bukatan kowa ya fadamata mai zatayi.

“Duk da haka maihaifiya ta ta taimaka min wajen zama abun da nakeso da fahimtar dani waye ni”.

Yaya iyayenki suka ji bayan kin nuna sha’awarki Akan waka da kuma Sana’ar:

Qing Madi: na tashi da mahaifiya ta, tayi murna sosai cewar adduar mu ya karbu.

Menene ya Baki basirar yin wakar See finish kuma ya kikaji da wakar ta samu shahara a Najeriya:

Qing Madi: Na samu basirar See Finish a zahirance ya faru dani, hakan ya kawo basirar kuma Naha hanya ce ta fadin zahirin rayuwa da kuma bayyana abubuwan da ke faruwa. Ina Jin wakar naji inyi wani abu akai.

Jin wasu suna fadin kalmomin wakar da nayi yasani ganin abu sabuwa. Naji dadi Saboda mutane dayawa sun fadamin wakar ta basu amsoshi da kwanciyar hankali.

Yaya kike sarrafa lokacin waka Dana karatu a matsayinki na matashiya:

Qing Madi: A yanzu ban fara jami’a ba, ina matukar aiki ne akan waka da kuma rayuwar matashiya.

Kinyi Waka a daya daga cikin manya event na kasar Homecoming event, menene kika fuskanta a karamin shekarun ki:

Qing Madi: Naji matukar dadi da karamci na samun wannan damar, hakan ya bani kusanci da mutane da kuma yi musu waka.

Da samun daukaka a karamin shekaru, me kikeyi yasaki kiji ki kamar yarinya:

Qing Madi: hira da babbar kawata yana taimaka min wajen ji na mai kamar yadda nake, hakan kamar magani ne a wuri na.

Me kike aiki akai yanzu kuma mai masu jinki zasu samu a wajenki da kuma nan gaba:

Qing Madi: ina aiki ne Akan wakoki a matsayina na mawakiya da sabuwar sauti da kuma waka da wasu. Ina farinciki kuma ina fatan magoya baya zasuyi farin ciki da hakan.

Hotunan Qing Madi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button