
Babban Lauya ya shigar da Gwamnatin tarayya kara a kotu yana neman ta biya diyyar Biliyan N1.5bn bisa yunkurin hana Zanga-Zanga
Lauyan ya shigar da qara kuma a cikiɲ ƙarar tasa sun haɗa da Gwamnatiɲ tarayya a matsayin wacce ake kara ta farko sai kuma mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokiɲ tsarò (NSA).
Karar tashi ya hada da Babban hafsan tsaro, babban hafsan soji, sojojin Nâjeriya, sufeto janar na ‘yan saɲdâ (IGP), rundunar ‘yan sandan Nâjeriya (NPF), Hukumar Tsârò ta farin kâya (DSS), da kuma Darakta Janar na Hukumar Tsaron Jihohi
A Yau Talata ne jami’inmu na Labaranyau yasamo rahoton cewa Olukoya Ogungbeje ya kai ƙarar ne a madadin kansa da daukacin yan Najeriya masu kishin kasa da ke neman shiga zanga-zangar lumana don samar da shugabanci na gari a Najeriya.
Kuma ya kara da cewa karar tana karkashin sashe na 33, 36, 38, 39, 40, da 46 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 wanda diyyarta yakai naira 1.2billion.
Yanzu haka Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 31 ga watan Yuli.
Menene ra’ayinu dan gane da wannan karar da aka kai na Gwamnatin Jaha da sauran manyan jiga jigan karar?