
Rundunar sojin Najeriya ta ce akwai makirce-makirce daga bangarori daban-daban na tunzura jami’an sojin Najeriya don hambarar da gwamnatin dimokaradiyya a yanzu.
Rundunar Sojan Najeriya ta ce akwai makirce-makirce daga bangarori daban-daban na tunzura jami’an Sojin Najeriya don hambarar da gwamnatin Dimokaradiyya da Shugaba Bola Tinubu ke jagoranta.
Sai dai ta ce yunkurin ba zai yi nasara ba, inda ta nanata cewa sojoji sun yi farin ciki kuma sun fi dacewa a karkashin mulkin dimokuradiyya, don haka ba za su shiga duk wani mataki na yin zagon kasa ga dimokuradiyyar Najeriya da aka samu gindin zama ba.
Daraktan yada labarai na tsaro, Tukur Gusau, Birgediya-Janar, wanda ya bayyana hakan a wani sakon farko da ya aike wa Aminiya a safiyar ranar Asabar, ya bayyana faruwar lamarin a matsayin rashin kishin kasa da mugunta.
A cewarsa, sojojin za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na tsarin mulkin kasar maimakon shirya duk wani juyin mulki ga gwamnatin dimokaradiyyar da ke yanzu, yana mai cewa sojojin Najeriya ba za su shagala ba.
Martanin Gusau ya biyo bayan kiraye-kirayen da wasu ‘yan Najeriya suka yi na cewa sojoji su shiga cikin shugabancin kasar sakamakon gazawar gwamnatocin dimokaradiyya.
Sai dai a cikin sakon nasa, babban hafsan sojan ya ce sojojin Najeriya karkashin jagorancin Janar Christopher Musa, babban hafsan tsaron kasar, ba za su shiga cikin kowane irin tada kayar baya ba.
“Rahotanni da ake kira ga sojoji da su tsoma baki cikin dimokuradiyyar mu, rashin kishin kasa ne, mugunta, da kuma yunkurin kawar da hankalin sojojin Najeriya daga gudanar da ayyukan da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su,” in ji babban sojojin.