Girke GirkeLabaran Hausa

Yadda Ake Girka Tuwon Dawa

Tuwon dawa tuwo ne na hausawa duk da dai wasu yankin fadin kasar najeriya ma an gano suna ci, ana cin ta da miya iri iri duk wanda rai  ya fi so.

Tuwon dawa yanada saukin sarrafawa, biyomu domin karanta yadda ake girka Tuwon Dawa.

Kayan Hada Tuwon Dawa

1. Nikeken garin dawa

2. Kanwa

3. Ruwa

Yadda Ake Girka Tuwon Dawa

  • Da farko zaki dora tukunyar a wuta asa ruwa daidai misali.
  • Idan ya tafasa sai a debo garin dawar da aka tankade asa ruwa a dama a zuba a kan tafasasshen ruwan.
  • Sai asa mucciya a juya don kar ya yi gudaje.
  • Sai akawo ruwan kanwa kadan a zuba a barshi yayi ta dahuwa.
  • Idan yayi sai a tuka za’a ga har yauki yake yi.
  • Idan an gama tukawa sai a rufe ya dan turara, za’a ji yana kamshi sai a malmala shi.
  • Zaki iya cin tuwon dawa da irin miyar da ki ke so, amma yafi tafiya da miyar kuka ko danyen kubewa.

Ga Bidiyon Yanda Ake Girka Tuwon Dawa

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button