Girke GirkeLabaran Hausa

Yadda Ake Girka Jollof Na Shinkafa Cikin karamin Lokaci

Shinkafa dai a kasar hausa Ana kiranta yar kullum, saboda mafi yawan gidaje cikin hausawa Ana dafa shin kafa kullum. Shinkafa ba abinci ne wanda ake saurin gajiya da ita ba.

Shinkafa Tana da nau’i daban na sarrafa ta, a yau dai zamu kawo miki yadda ake sarrafa Shinkafa wato Jollof. In kin bi yadda muka nuna miki a nan bara aji kunya ba.

Jollof Rice
Jollof Rice

Kayan Hadin Jollof Rice

1. Shinkafa

2. Tattasai

3. Attaruhu

4. Albasa

5. Citta

6. Tafarnuwa

7. Maggi

8. Gishiri

9. Man gyada ko manja

10 Nama ko kifi

Yadda Ake Girka Jollof Rice

  • Da farko za’a saka ruwa a wuta sai yayi zafi sosai sai a zuba Shinkafa
  • Sai a kulle tukunyar a kalla na minti goma sha biyar.
  • Sai a sauke a wanke a ajiye a gefe.
  • Dalilin wanke war saboda a rage starch din da yake cikin shinkafar saboda kar ya mai da shinkafar kamar gwate gwate.
  • Sannan a tafasa namanki indan an wanke namar a zuba kayan miya wanda aka jajjaga albasa, tafarnuwa, citta da attaruhu da dan maggi ko onga haka a ajiye a gefe.
  • Sai a soya manja ko man gyada, a zuba jajjagen tattasai dasu albasa da attaruhu da citta da tafarnuwa.
  • Sai a soya shi, A tsame namar cikin ruwan namar da aka tafasa ahada aciki su soyu tare da kayan miyan.
  • Sannan a zuba maggi da gishiri sai a juye ruwan namar.
  • In anaso akara curry da thyme, amma in ba halin hakan ba dole bane.
  • Sai akara ruwa yanda zai karasa dafa namar in ruwan namar bare kai ba.
  • A rufe shi ya tafasa kamin a zuba shinkafar.
  • Bayan minti goma sha biyar in akan gas ne na tabbata abincin ya Jallof Rice ya dahu.

Sai ki sauke a zuba aci Jollof din shinkafa mai Dadi.


Discover more from Labaran Yau

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Discover more from Labaran Yau

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading