Hali Ko Yanayin Rayuwa?: Abin Mamaki A Makabartan Bauchi
Abin mamaki a makabartan Bauchi, shin jama’a wannan dame zaku kirashi, abun da yakamata ayi salati ne, in an duba abun ta wani fuska, sai ya dawo abun mamaki.
Wani matashi ya bayyana bakin cikin shi ganin yanda yanayin makabartan dake kwaryan garin Bauchi ke ciki na rashi da karancin kayan aiki masu inganci. Matashin ya tsinci kansa a tawagan raka wata gawa a kwanaki kadan da suka wuce a wannan sabuwan shekara namu na 2024.
Matashin ya bayyana zuciyansa ne a shafinsa na yanan gizo na facebook wanda Labaranyau media ta kasance me cikin nasaran tabbatar da wannan labari. Ance waka a bakin meshi tafi dadi, to bari kuji daga gurin asalin me sakon a shafin yanansa na facebook.
Kadan daga cikin hotunan da suka samu a wurin da kuma daidai lokacin da abun ya faru. Ka duba a hankali ka gani.