Labaran TuranciNEWS

Sabon Hari – Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 40

Sabon Hari – Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 40

 Mutane 40 ne suka rasa rayukansu awani hari da aka kai a garin giwa dake jihar kaduna dake arewa masu yamma na Nigeria. 

Maharan sun kai hare-haren ne a garuruwa daban-daban na ƙaramar hukumar Giwan.

Wannan na zuwa ne bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai a filin jirgin sama na Kaduna a ranar Asabar ɗin da ta wuce, inda suka kashe a ƙalla ma’aikata biyu na filin jirgin.

Tuni aka yi jana’izar waɗanda aka kashe ɗin a wasu garuruwan na yankin Giwan amma har yanzu a wani garin ba a yi zana’izar mutanen da suka mutu ba.

Wani magidanci daga garin Tsaunin-Mayau da yanzu haka ke gudun hijira a wani garin bayan ya ƙetare rijiya da baya ya yi wa manema labarai karin bayani.

Kashe mu suke yi kamar suna kashe kiyashi. Da ƙarfe hudu na yamma suka dirar mana, a ƙalla ba a ƙasara ba sun zo da babur ya kai 300.

Sun kashe mutum 14 nan take a gidana, gawarwakin ma suna nan ba a kwashe su ba, ba a yi jana’izarsu ba.

“Ba a yi jana’ziarsu ba don kowa ya gudu ana tsoron cewa za su dawo su sake kashe mutane, duk garin ya tarwatse.

Tsaknain garuruwan nan uku akwai mutum sun fi dubu ɗaya tsakanin mata da maza da yara. Hanyar cike take da ɗan adam, suna nan kowa a ƙafa yake tafiya.

A yanzu haka hare-haren da ake yawan kai wa jihohin Zamfara da Neja masu maƙwabtaka da Kadunan sun sa mutune barin garuruwansu.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button