
Man City Sun Sayi Nunes Daga Wolves A Kudi £53m
Matheus Nunes zai tafi Manchester City daga Wolves a £53m, zai zama dan wasa me tsada da Wolves suka taba sayarwa a gaba tarihin saye-sayen su.

Nunes yana daya daga cikin yan wasan da Man City suke nema a wannan Transfer Window din, bayan zuwan Josko Gvardiol, Mateo Kovacic da kuma Jeremy Doku, wadda kudin su gaba daya yakai £216.1m wannan Transfer Window.
Josko Gvardiol

Mateo Kovacic

Jeremy Doku

Man City suna neman dan wasan dazai buga wajen Kevin De Bruyne bayan tafiyar sa injury na watanni a wasan su da suka buga da Burnley na farkon Premier League.
Nunes ya tafi yajin aiki a lokacin da aka kusa rufe Transfer Window saboda son tafiya Etihad domin buga wasa a Man City.