Labaran Turanci

Jami’in Bayyana Sakamakon Zabe Farfesa Ibrahim Yakasai Ya Rubutawa Komishina Cewa…

Rashin tabbas a kadarar Dan Majalisa Doguwa

Dan takarar majalisan tarayya na jam’iyyar kayan marmari NNPP, na Tudunwada/ Doguwa mazabar tarayya, Salisu Yushau ya kai kara wajen kotun dake duba wajen Gudanar da zaben yan majilisun jiha da na tarayya wanda keh zama a Kano.

Dan takaran na neman hukumar zabe ta tsaida zaben da za a maimaita na yan majalisun a mazabar.

Jagoran cikin gida a Majalisan tarayya Ado Doguwa ya kasance shine zababben dan majalisan a zaben da ta gabata na ran 25 ga watan fabrailu a mazabar, Kamin hukumar zabe ta INEC ta janye sakamakon zaben akan Sai an sake yi.

Jami’in bayyana sakamakon zabe, farfesa Ibrahim Yakasai ya rubuta wa kwamishinan zabe na kano, Abdul Zango ya fadamai cewa ya bayyana sakamakon zaben ne dan an tilasta mai.

Dokar zabe ta 2022 ta bayyana, hukumar tanada karfin duba cikin Al’amuran zabe cikin kwana bakwai koh ansa tilasci wajen bayyana sakamakon zabe koh anyi cin zarafi. Hakan dokar zabe ne.

A Takardar wanda tazo ran uku ga watan hudu zuwa ga shugaban hukumar zabe Mahmoud Yakubu, lauyan meh Karar, Adegboyega Awomolo, ya janye hankalin hukumar zabe dan ta tsayar da maimaicin zaben da zata gudanar.

Lauyan yana Jan hankalin su tsayar saboda dan takarar majalisan tarayya na jam’iyyar NNPP ya kai kara kotu. Sai kotu ta yanke hukunci Kamin hukumar zabe ta dau mataki na gaba.


Discover more from Labaran Yau

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Discover more from Labaran Yau

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading